Masarautun Kano: Kotu Ta Sanya Lokacin Fara Sauraran Shari'a, Ta Fadi Ka'idar Zama
- Babbar Kotun Tarayya da ke jihar Kano ta shirya fara sauraran shari'ar da aka shigar kan masarautun jihar
- Kotun ta sanya yau Alhamis 6 ga watan Yuni domin fara sauraran karar da aka dage saboda yajin aikin kwadago
- Hakan ya biyo bayan maka Gwamna Abba Kabir a kotu bayan rushe masarautun da gwamnatin Abdullahi Ganduje ta kirkiro
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Kotu ta sanya ranar fara sauraran shari'ar da aka shigar kan rigimar masarautun jihar Kano.
Kotu ta zabi yau Alhamis 6 ga watan Yuni domin sauraren shari'ar ta manhajar Zoom.
Kano: Kotu ta fara zama kan masarautu
Babbar Kotun Tarayya da ke Jihar Kano karkashin jagorancin Mai shari'a, A.A Liman za ta fara jin bahasin bangarorin biyu, cewar Aminiya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Idan ba ku manta ba, kotun ta sanya Litinin 3 ga watan Yuni a matsayin ranar fara sauraran karar wadda aka dage sakamakon yajin aikin kungiyoyin Kwadago.
Daya daga cikin manyan hakimai a fadar Kano, Sarkin Dawaki Babba, Alh. Aminu Babba Dan Agundi wanda kuma Hakimin Nassarawa ne shi ya shigar da karar a gaban kotun, cewar New Telegraph.
An maka Majalisa, gwamnan Kano a kotu
Dan Agundi yana kalubalantar Majalisar Dokokin jihar da Gwamna Abba Kabir kan rushe masarautun jihar 5 da gwamnatin Ganduje ta kirkiro.
Hakan ya biyo bayan tabbatar dadakiar rushe masarautun da Majalisar jihar ta yi yayin da Abba Kabir yasa ya mata hannu.
Daukar wannan mataki ya kawo rigima a jihar kan ainihin wanene sahihin sarki tsakanin Aminu Ado Bayero da kuma Muhammadu Sanusi II.
An dage zaman shari'ar masarautun Kano
A wani labarin kun ji cewa yajin aikin da ma'aikata suka fara yau Litinin 3 ga watan Yuni ya kawo tsaiko a ci gaba da sauraron shari'a kan masarautar Kano.
Manyan ƙungiyoyin kwadago na ƙasa NLC da TUC sun shiga yajin aikin sai baba-ta-gani biyo bayan gaza cimma matsaya kan mafi ƙarancin albashi da ƙarin kuɗin wuta.
Hakan ya biyo maka Majalisar jihar da Abba Kabir da aka yi kan rushe masarautu biyar da gwamnatin Abdullahi Ganduje ta kirkiro.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng