NLC Na Neman Ƙarin Albashi, Tinubu Ya Bayyana Wani Muhimmin Aiki da Zai Yi Zuwa 2030
- Shugaba Bola Tinubu ya sha alwashin dasa itatuwa miliyan 25 a cikin shekara shida yayin da ake bikin ranar muhalli ta duniya
- Shugaban kasar ya ce zai gina 'birnin tsirrai', irinsa na farko a Najeriya da nufin zama cibiyar kare muhalli a yankin Afrika
- Wannan na zuwa ne yayin da 'yan kwadago suka tsagaita yajin aikin da suke yi da tunanin cimma matsaya kan mafi ƙarancin albashi
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya yi alkawarin cewa gwamnatin Najeriya za ta dasa bishiyoyi miliyan 25 daga nan zuwa shekarar 2030.
Wannan na zuwa ne yayin da kungiyoyin kwadago na NLC da TUC suka janye yajin aiki a kokarin cimma matsaya kan mafi ƙarancin albashi.
Shugaba Tinubu ya kuma ba da tabbacin cewa zai samar da damarmaki ga matasan Najeriya a fannin shuke shuke da ci gaban muhalli.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bikin zagayowar ranar muhalli ta duniya
Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, Tinubu ya yi kira ga masu ruwa da tsaki da su zage dantse wajen kare muhalli a yunkurin samar da tattalin arziki mai tsafta.
Shugaban kasar ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a lokacin da ya ke fitar da sakon bikin zagayowar ranar muhalli ta duniya.
Majalisar Dinkin Duniya ce ta kirkiri ranar muhalli ta duniya a wani taron Stockholm kan muhalli a shekarar 1972.
Tinubu: "Najeriya za ta gina 'birnin tsirrai'"
Shugaban kasar ya ce taken bikin ranar na wannan shekarar, 'Dawo da martabar ƙasa, yaki da fari da kwararowar hamada' ya shafi kasar Najeriya kai tsaye, in ji rahoton The Cable.
A cikin wata sanarwa da Ajuri Ngelale, mai magana da yawun shugaban kasa ya fitar, Tinubu ya ba da umarnin gina 'birnin tsirrai' na farko a Najeriya.
Idan aka kammala ginin birnin, zai zama wata cibiya mai karfi a Afrika da za a rika samar da fasahar makamashi mai dorewa da kuma magance matsalolin muhalli da na yanayi.
'Yan kwadago sun janye yajin aiki
Tun da fari, mun ruwaito cewa 'yan kwadagon Najeriya da suka hada da kungiyar NLC da TUC sun janye yajin aikin sai baba ta gani da suka shiga.
Wannan na zuwa ne bayan kungiyoyin da gwamnatin tarayya sun yi wani zama tare da cimma yarjejeniya kan duba mafi ƙarancin albashi da zai dace da ma'aikata a yanzu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng