Majalisar Dinkin Duniya ta ce Talakawa sun fi attajirai kashe kudi wurin samun ruwa
A wani rahoto da sashin majalisar dinkin duniya ta gabatar, ta ce talakawa a sassa daban-daban na duniya sun fi attajirai kashe kudi wurin samun ruwa.
Majalisar ta bayyana hakan ne a ranar Talata a inda ta ce akalla mutane biliyan 2.1 su ke fama da karancin tsabtatacen ruwan sha. Rahoton ya dada da cewar fiye da mutane biliyan 4.3 ba su da tsabtataccen muhalli wanda jigo ne na cigaba da zaman lafiyar al’umma.
A cewar majalisar, rashin magance matsalar samar da ruwa zai iya haifar da karancin abinci da rugujewar tattalin arziki ya zuwa sheakar 2050.
KU KARANTA: Dalilin da yasa ban goyi bayan kowane dan siyasa ba - Nafis Abdullahi
Rahoton ya kuma bayyana cewar kudin da talakawa ke kashewa wurin sayan ruwa ya ninka kudin da attajirai ke biya na ruwan famfo sau goma zuwa ashirin. Don haka ne ya ce maganar talakawa ba za su iya biyan kudin ruwan famfo ba, kuskure ne.
Afirika c eke da kaso mafi tsoka na wannan matsala ta ruwa a inda kasha 24 cikin dari ke samun tsabtacaccen ruwan sha.
Ita kuwa Kungiyar Kiwon Lafiya ta Duniya (WHO), ta ce kimanin yara 1000 ne ke halaka a kullum sakamakon gurbataccen ruwan sha. Bugu da kari, matan aure da ‘yan mata sun a bata lokaci ma su muhimmanci wurin debo ruwa daga wurare ma su nisa a kullum.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.nag Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng