Majalisar Dattawa na Neman Tsaurara Hukuncin Rashin Tura Yara Makaranta
- Majalisar dattawan Najeriya za ta samar da dokar da za ta tsaurara hukunci kan iyayen da ba su tura yaransu makaranta duk da cewa akwai dokar ilimi dole kuma kyauta
- Sanata Idiat Adebule ta bijiro da kudirin da ake son a kara kudin tara da ake karba a hannun iyaye da ba su kai yara karatu a jihohi da birnin tarayyar Abuja
- A zaman majalisar na Laraba, an amince da kudirin dokar da za ta bayar da damar yiwa dokar ilimin bai daya kwaskwarima, inda za a ci tarar N250,000 maimakon N2500
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. Abuja- Majalisar dattawan Najeriya ta nemi gwamnati ta dauki tsattsauran mataki kan iyayen dake barin yaransu na gararanba a kan titi maimakon zuwa makaranta. 'Yan majalisar na neman a kara tarar da ake cin iyayen da ke kin sa yaransu a makaranta sosai.
Channels Television ta wallafa cewa a zaman majalisar na Larabar nan, an nemi a kara tarar zuwa N250,000 daga N2,500 da aka gindaya a baya.
Majalisa za ta tilasta kai yara makaranta
A zaman majalisar, an zartar da kudirin gyara dokar tilastawa iyaye kai yaransu makaranta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kudirin da Sanata Idiat Adebule ta gabatar zai yiwa dokar ilimin bai daya kwaskwarima ta yadda za a ba jihohi da gwamnatin tarayya damar gurfanar da iyaye gaban kotu idan sun ki tura yaransu karatu. Kudirin dokar ya yi bayanin cewa duk wadanda suka ki kai yaransu makaranta za a tuhuma, kamar yadda ta dade yana son yi, kamar yadda The Nation ta wallafa. Amma ta ware iyayen da ke zaune a kasar waje, inda ta ce dokar ba za ta yi aiki a kansu ba.
'Gwamnati ta fara gyarawa,' Masaniyar Ilimi
Shugabar sashen kula da bangaren ilimin 'ya'ya mata a ma'aikatar ilimi ta Kano, Hajiya Amina Kassim, ta ce gwamnati ce ya kamata ta fara daukar matakin zamanantar da makarantu. Ta shaidawa Legit Hausa cewa babu yadda za a yi yara su je makaranta cikinsu da yunwa, kuma babu ajujuwa, babu kujerun zama. Amina Kassim na ganin idan har gwamnati ta sauke nauyin dake kanta na gyara ilimi, ba sai an fitar da irin wannan dokar ba. Ta shawarci mahukunta su tabbatar da gyara tsarin ilimi sannan a samar da malamai domin dorewar ilimi.
Shugaba Bola Tinubu ya ki zuwa majalisa
A baya mun kawo muku labarin cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ki bayyana gaban majalisa kamar yadda aka yi alkawari zai yi.
Shugaban majalisar wakilai, Tajuddeen Abbas ya dora laifin hakan kan majalisa, inda ya ce bai kamata su gayyaci shugaban kasar ba domin sai 12 Yuni 2024 zai yi jawabi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng