Atiku Ya Ragargaji Tinubu Bayan Tabbatar da Dawo da Tallafin Man Fetur a Ɓoye

Atiku Ya Ragargaji Tinubu Bayan Tabbatar da Dawo da Tallafin Man Fetur a Ɓoye

  • Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya yi magana kan yadda Bola Ahmed Tinubu ya ke jagorantar Najeriya
  • Atiku Abubakar ya ce akwai lauje cikin naɗi kan yadda Bola Tinubu ya gaza yiwa ƴan kasa bayani kan lamarin tallafin man fetur
  • Ya ce Najeriya ba za ta taɓa cigaba ba idan dai Tinubu zai cigaba da yiwa kasar tuƙin ƴan koyo kuma yana nuna cewa ya ƙware

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nigeria - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya caccaki Tinubu kan yadda yake tafiyar da mulkin Najeriya.

Atiku Abubakar ya bayyana cewa akwai tarin matsaloli da suka dabaibaye tattalin arzikin kasar da Bola Tinubu ya ki bayyanawa.

Kara karanta wannan

"Yadda Tiinubu yake biyan tallafin fetur bayan sanar da soke tsarin tun ranar farko"

Atiku da Tinubu
Atiku ya zargi Tinubu da dawo da tallafin mai a boye. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Atiku Abubakar
Asali: Facebook

A cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Atiku Abubakar ya ce cikin abubuwan da Tinubu ya ki bayyanawa akwai dawo da tallafin mai a sirrance.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Atiku: "Muna son bayani kan tallafin man fetur"

Atiku Abubakar ya bayyana cewa tun kwanaki ya bukaci shugaba Bola Tinubu ya fito ya bayyanawa yan Najeriya yadda ake ciki bayan ya cire tallafin fetur.

Ya ce akwai bukatar yan Najeriya su san ina kudaden tallafin suka shiga kuma wane cigaba aka samu bayan cire tallafin amma abin ya gagara.

Kudin tallafin man fetur ya karu

Atiku Abubakar ya ce ana cikin bukatar sanin kudin da gwamnati ta tara bayan cire tallafi sai aka ji kudin tallafin da gwamnati ke kashewa ya karu.

Tsohon shugaban kasar ya ce a shekarar 2023 an kashe Naira tiriliyan 3.6, sannan bayan Tinubu ya 'cire' tallafi kuma an kashe Naira tiriliyan 5.4 a 2024.

Kara karanta wannan

'Yan kwadago: Shugaba Tinubu ya dauki matakin gaggawa domin hana yajin aiki

Atiku ya ce Najeriya na tafiya a bai-bai

Saboda haka Atiku ya ce Najeriya ba ta tafiya a saiti ƙarƙashin Tinubu kuma akwai bukatar ya yiwa ƴan ƙasa gamsasshen bayani.

Atiku ya ce Bola Tinubu ya dawo da tallafi a boye amma kuma kullum yana cewa ya cire tallafi saboda tukin ƴan koyo yake.

Atiku Abubakar ya gana da Peter Obi

A wani rahoton, kun ji cewa manyan ƴan takarar shugaban ƙasa a 2023, Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na LP sun gana yayin da ake shirin zaɓen 2027.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku ya ce abin alfahari da girma ne da ya karɓi bakuncin tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel