Rundunar 'Yan Sandan Kano Ta yi Namijin Aiki, an Damke Miyagu Iri Iri

Rundunar 'Yan Sandan Kano Ta yi Namijin Aiki, an Damke Miyagu Iri Iri

  • Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta bayyana cewa ana samun nasara wajen yakar ta'addanci da kawar da ayyukan bata-gari a fadin jihar
  • Jami'in hulda da jama'a na rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya tabbatar da bayan an yi holensu a babban ofishin 'yan sanda
  • Daga laifuffukan da ake zargin matasan da aikatawa akwai fashi da makami, garkuwa da mutane da satar shanu, kuma an kwato makamai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano- Rundunar yan sandan Kano ta cafke wasu mutane 19 da ake zargi da aikata mugayen laifuka a jihar. Daga irin laifukan da ake zarginsu da aikatawa akwai satar mutane, fashi da makami, satar shanu da sauran miyagun ayyuka a jihar.

Kara karanta wannan

NSCDC a Kano ta damke masu addabar al'ummar jihar da sace-sace

SP Abdullahi Kiyawa
'Yan sanda a Kano sun cafke miyagu 19 Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Asali: UGC

A sakon da jami'in hulda da jama'a na rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya sanya a shafinsa na facebook, ya ce tuni aka yi holin matasan da makaman da aka kwato a hannayensu.

Wadanne makamai 'yan sanda suka samu?

Jaridar Nigerian Tribune ta wallafa cewa rundunar 'yan sandan ta yi nasarar karbe mugayen makamai daga wurin bata-garin. Daga makaman da aka samu akwai bindigogi kirar AK47 guda biyu, da kirar Pistol mai hayaki guda daya, sai kuma harsashi guda 26. An kuma samu wasu bindigogin, da motoci guda biyu sai raguna 28, kamat yadda SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan sandan Kano sun nemi taimako

Rundunar 'yan sandan Kano ta nemi taimakon jama'ar gari su taimaka mata wajen ganin an cimma nasara kan yakar ta'addanci.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, CP Muhammad Usaini Gumel ya nemi tallafin, inda ya yi alkawarin za su ci gaba da tsare rayukan jama'a.

Kara karanta wannan

Rundunar 'yan sandan Kano ta baza komar kama masu kokarin dawo da fadan daba jihar

Ya ce za ta gurfanar da wasu fitinannun matasa 19 da ta kama gaban kotu domin su girbi abin da suke shukawa a cikin al'umma.

'Yan sandan Kano na neman 'yan daba

A wani labarin mun ji cewa rundunar 'yan sandan jihar Kano ta fara neman wasu iyayen daba 13 ruwa a jallo bayan gano rawar da suke takawa kan rashin tsaro.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya tabbatar da neman da ake yi musu, inda ya yi zargin suna kokarin dawo da fadan daba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.