Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum Ya Rasu? Gaskiya Ta Bayyana

Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum Ya Rasu? Gaskiya Ta Bayyana

  • An wayi gari yau da jita jitar cewa Allah ya yiwa babban malamin addinin Musulunci Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum
  • Ana cikin haka Sheikh Ahmad Tijjani Guruntum ya ƙaryata rade-radin bayan al'ummar Musulmi sun fara shiga alhini
  • Duk da haka, Malamin ya bayyana gaskiyar abin da ya faru wanda shi ne ya jawo mutane suka fara yaɗa jita jitar a safiyar yau

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Bauchi - A yau Laraba, 5 ga watan Yuni mutane suka fara yaɗa jita jitar cewa Allah ya yiwa Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum rasuwa.

Masu ƴada jita jitar suna rubutu ne tare da sanya hoton wata mota da ake ganin tana da alaka da malamin.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da rigimar sarautar Kano, Sarki Sanusi II ya faɗi abin da zai kawo ci gaba a ƙasa

SHeikh Guruntum
Sheikh Guruntum ya karyata cewa ya rasu. Hoto: Mallam Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum
Asali: Facebook

Sai dai Sheikh Guruntum ya bayyana gaskiyar abin da ya faru a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ɗan Sheikh Guruntum ya yi hatsari

Sheikh Guruntum ya bayyana cewa asalin abin da ya faru shi ne yaronsa ne ya yi hatsari sai mutane suka rika ɗaukan hoton motar suna cewa shi ne ya mutu.

Duk da haka malamin ya bayyana cewa yaron na shi yana cikin koshin lafiya saboda bai ji rauni ba a sanadiyyar haɗarin.

Sheikh Guruntum ya yi nasiha

Biyo bayan yada jita jitar malam ya mutu, ya karyata labarin tare da yin nasiha ga masu ƴaɗa labarin ƙanzon kurege.

Malam Guruntum ya ce ya kamata mutane su nisanci yada abin da ba su da tabbas da cewa ya faru.

A karshe malamin ya yi kira ga al'ummar Musulmi da su kwantar da hankulansu domin komai yana tafiya daidai tattare da rayuwarsa.

Kara karanta wannan

Matawalle ya dauki zafi kan kisan sojoji a Abia, ya fadi matakin dauka

Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum shahararren malamin addinin Musulunci ne da ya fito daga jihar Bauchi.

Izala ta kai dan agaji zuwa Hajji

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kungiyar Jama'atu Izatil Bidi'a Wa Ikamatis Sunnah, Sheikh Abdullahi Bala Lau ya kai dan agaji Hajji.

Sheikh Abdullahi Bala Lau ya yi alkawarin kai dan agajin zuwa Hajji ne yayin da ya tsinci makudan kudi kuma ya maido su ga mai su.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel