El Rufai Ya Tafka 'Aika Aika': Ana Zargin Tsohon Gwamna Ya Karkatar da N423bn

El Rufai Ya Tafka 'Aika Aika': Ana Zargin Tsohon Gwamna Ya Karkatar da N423bn

  • Kwamitin da majalisar Kaduna ta kafa domin bincikar ayyukan gwamnatin Nasiru El-Rufai ya nemi a gurfanar da tsohon gwamnan
  • Kwamitin ya ce ya gano tsohon gwamnan na Kaduna ya ci zarafin ofis, ya karkatar da kudin jama'a da kuma ranto kudi masu yawa
  • Da ya ke karbar rahoton, kakakin majalisar jihar, Yusuf Liman ya ce ana zargin gwamnatin El-Rufai ta karkatar da Naira biliyan 423

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Kaduna - Kwamitin wucin gadi da majalisar Kaduna ta kafa domin bincikar basussuka da kwangilolin da tsohon gwamnan jihar, Nasiru El-Rufai ya mika rahotonsa.

Malisar Kaduna ta yi magana kan tuhumar El-Rufai
Kaduna: Kwamiti ya gano aika-aikar da gwamnatin El-Rufai ta yi. Hoto: @elrufai
Asali: Facebook

Shugaban kwamitin, Henry Zacharia ne ya mika rahoton a zaman majalisar na ranar Laraba. Ya ce gwamnatin El-Rufai ta yi aika-aika kafin barin mulki.

Kara karanta wannan

Kaduna: An shiga tashin hankali, wata amarya ta datse mazakutar angonta

"El-Rufai ya karkatar da N423bn" - Liman

Henry Zacharia ya ce El-Rufai bai bi ƙa'ida wajen bayar da wasu kwangiloli ba sannan wasu basussukan ba a yi amfani da su yadda ya dace ba, in ji rahoton Channels.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da ya ke karbar rahoton, kakakin majalisar Kaduna, Yusuf Liman ya ce ana zargin gwamnatin Malam Nasiru El-Rufai ta karkatar da Naira biliyan 423 tare da barin tarin bashi.

Kwamitin wucin gadin ya ba da shawarar a tuhumi El-Rufai tare da gurfanar da shi a gaban kotu da shi da wasu 'yan majalisar gwamnatinsa.

Kwamitin ya ce jami'an tsaro da hukumomin yaki da rashawa su tuhumi tsohon gwamnan kan cin zarafin ofis, karkatar da kudi da kuma ranto kudi masu yawa ba tare da dalili ba.

Kwamitin ya nemi a kori kwamishinan El-Rufai

Kara karanta wannan

Gwamnatin Gombe za ta yi titin da kilomita 1 zai lakume sama da Naira biliyan 1

Jaridar The Punch ta ruwaito kwamitin ya kuma ba da shawarar a kori kwanishinan kudi na jihar Kaduna, Shizer Badda wanda ya taba yin aiki a karkashin gwamnatin El-Rufai.

Haka zalika kwamitin ya nemi a sallami shugaban hukumar ilimin bai daya ta jihar, da gudanar da kwakkwaran bincike kan wasu nade-nade da gwamnatin El-Rufai ta yi.

Majalisar Kaduna za ta binciki El-Rufai

Tun da fari, mun ruwaito cewa majalisar dokokin jihar Kaduna ta kafa kwamitin wucin gadi da zai binciki bayanin basussuka, tallafi da ayyukan da gwamnatin Nasir El-Rufai ta yi daga 2015 zuwa 2023.

Kafa kwamitin mai mutum 13 na zuwa ne bayan da Gwamna Uba Sani ya ce gwamnatinsa ta gaji bashin $587m da kuma N85bn, tare da kwangiloli 115 daga gwamnatin El-Rufai.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel