Gwamnatin Niger ta Bayyana Abin da ke Kawo Cikas Wajen Ceto Wadanda Gini Ya Rufta Musu
- Gwamnatin jihar Niger ta bayyana matsalar tsaro da babban kalubalen da ke dakile yunkurin ceto wadanda kasa ta danne a mahakar ma'adanai a jihar
- Mutane 30 zuwa 50 ne ake fargabar kasa ta danne lokacin da suke tsaka da aikin hakar ma'adanai a yankin Galadima-Kogo dake karamar hukumar Shiroro
- Kwamishinan bayar da agaji da kula da iftila'i a jihar, Ahmed Baba Suleiman Yumu ya ce duk da kokarin da suke yi wajen ceton rai, hare-haren 'yan ta'adda na kawo cikas
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Niger- Gwamnatin jihar Niger ta dora laifin gaza ceto wadanda suka makale a karkashin mahakar ma'adanai kan rashin tsaro da ya addabi yankin Galadima-Kogo da abun ya faru.
A jiya ne wata mahakar ma'adanai dake karamar hukumar Shiroro a jihar ta rufta yayin da ake zaton akwai wasu mutane 30 da ta danne a karkashin kasa.
Daily Trust ta tattaro cewa kwamishinan jin kai da kula da iftila'i a jihar, Ahmed Baba Suleiman Yumu ne ya tabbatarwa da manema labarai matsalar da ake fuskanta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An rasa rai a mahakar ma'adanan Niger
Mutane 30 ne ake fargabar za su iya rasa rayukansu a karkashin mahakar ma'adanai da ke Galadima Kogo a jihar Niger.
Duk da rahotanni sun tabbatar da mutuwar mutum daya, ana fargabar rashin agaji a kan lokaci kan iya yin sanadiyyar rasuwar sauran da ke makale a karkashin kasa.
An samu mabanbantan alkaluma kan adadin mutane da ginin ya danne, inda Vanguard News ta wallafa cewa akalla mutane 50 ne a karkashin kasa.
Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa na jihar Niger, Abdullahi Baba Arah ya kuma bayyana cewa hukumar ba ta samu cikakkun bayani kan adadin da aka ceto ba saboda rashin tsaro a yankin.
Babban daraktan, ya ce hukumar ta samu rahoton yadda ’yan bindiga ke kai hare-hare a yankunan Shiroro da Mashegu a jihar.
'Yan bindiga sun sace mutane a Niger
A baya mun ruwaito muku cewa 'yan ta'adda sun kutsa wasu kauyuka guda biyu a jihar Niger, sun sace mutane da dama domin neman kudin fansa.
Shugaban karamar hukumar Munya, Aminu Najume ya tabbatar da cewa 'yan ta'addar sun shiga kauyukan Munya da Tunga inda suka sace mutane 56.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng