Rahoto: Yajin Aikin ’Yan Ƙwadago Ya Jawo Najeriya Ta Yi Asarar Naira Biliyan 149

Rahoto: Yajin Aikin ’Yan Ƙwadago Ya Jawo Najeriya Ta Yi Asarar Naira Biliyan 149

  • Sakamakon yajin aikin kwana ɗaya da kungiyoyin kwadago suka shiga a ranar Litinin, ana hasashen Najeriya ta yi asarar kudi har N149bn
  • A ranar Litinin, ma'aikatan da ke aikin mai a kasar sun shiga yajin aiki tare da rufe dukkanin wuraren hako mai da sarrafa shi a fadin kasar
  • Hakan ya jawo Najeriya ba ta iya samun damar hako ganga 1,281,478 na danyen mai da ta saba haka a kullum ba, wanda kudinsa ya kai N149bn

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Ana hasashen Najeriya ta yi asarar akalla Naira biliyan 148.8 na harajin mai a ranar Litinin sakamakon yajin aikin 'yan kwadago.

Najeriya ta tafka asara a yajin aikin 'yan kwadago
Ana hasashen Najeriya ta yi asarar Naira biliyan 149 a ranar Litinin. Hoto: @NLCHeadquarters
Asali: Facebook

Yajin aiki: Najeriya ta yi asarar N149bn

Kara karanta wannan

Kaduna: An shiga tashin hankali, wata amarya ta datse mazakutar angonta

A cewar wani rahoton hukumar haƙo man fetur (NUPRC), Najeriya na samar da gangar danyen mai 1,281,478 a kowace rana.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ranar Litinin, an sayar da gangar mai na Brent a kan dala 78.27 yayin da bankin CBN ya ba da canjin dala 1 a kan N1,483.5, in ji rahoton The Punch.

Idan aka lissafa N1,483.5 sau adadin gangar mai da kasar ke fitar wa kullum wanda ma'aikatan hakar man ba su yi aiki ba a Litinin, za a ga yawan biliyoyin Naira da aka yi asara.

Kungiyoyin ma'aikatan mai sun shiga yajin aiki

Ma'aikatan mai karkashin kungiyar PENGASSAN da takwarorinsu na NUPENG da NGW sun rufe dukkanin injunan haƙo mai da ke a fadin kasar a yayin yajin aikin.

A ranar Lahadi, NLC ta umarci dukkanin 'yan kungiyar PENGASSAN da NUPENG da su rufe kafatanin wuraren hako mai a ranar Litinin in ji rahoton Channels.

Kara karanta wannan

Kungiyar ƙwadago ta janye yajin aiki, ta ba gwamnatin tarayya wa'adin mako 1

Majiyoyi a fannin mai na kasar sun tabbatar da cewa ma'aikatan sun rufe wuraren hako mai a ranar Litinin, lamarin da ya jawo aikin mai ya tsaya.

'Yan kwadago sun janye yajin aiki

A wani labarin, mun ruwaito cewa kungiyoyin kwadagon Najeriya da suka hada da NLC da TUC sun dakatar da yajin aikin da suka shiga.

'Yan kwadagon sun shiga yajin aiki ne a ranar Litinin saboda nuna adawa da gazawar gwamnatin tarayya na amincewa da sabon mafi karancin albashi da kuma janye karin kudin wutar lantarki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.