TCN Ya Kammala Gyaran Wuta a Arewa Maso Gabas Bayan Kwanaki Babu Lantarki

TCN Ya Kammala Gyaran Wuta a Arewa Maso Gabas Bayan Kwanaki Babu Lantarki

  • Kamfanin kula da rarraba wutar lantarki na kasa (TCN) ya sanar da kammala gyaran wutar lantarki a yankin Arewa maso gabas
  • A yau Talata, 4 ga watan Yuni kamfanin ya fitar da sanarwar kammala gyaran wanda ɓata gari suka lalata a tsakanin Gombe da Jos
  • Legit ta tattauna da Ahmad Murtala domin jin yadda yanayin wutar lantarki ta ke jihar bayan kammala gyaran da TCN ta yi

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Arewa - Kamfanin rarraba wutar lantarki na kasa (TCN) ya sanar da kammala gyaran wutar lantarki a Arewa maso gabashin Najeriya.

A yau Talata kamfanin ya ba da sanarwar cewa tun jiya Litinin, 3 ga watan Yuni ya kammala hada manyan layukan wutar.

Kara karanta wannan

NLC na neman ƙarin albashi, Tinubu ya bayyana wani muhimmin aiki da zai yi zuwa 2030

TCN AREWA MASO GABAS
TCN ya sanar da kammala gyaran wuta a Arewa maso gabas. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Kamfanin ya sanar da kammala aikin ne a shafinsa na Facebook in da ya ce ya kammala gyaran turakan wuta hudu da babban layin wuta daya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yaushe wutar lantarki za ta dawo yankin?

Duk da cewa kamfanin bai ayyana ranar da wutar za ta dawo ba, ya ce a yanzu haka suna shirye su fara aika lantarki ga yankin.

Saboda haka ake sa ran dawowar wutar lantarki a yankin a kowane lokaci daga sa'ar da kamfanin ya fitar da sanarwar.

Me ya kawo jinkirin gyaran wutar lantarki?

Tun ranar 22 ga watan Afrilu da aka lalata turakan wutar, kamfanin ya duƙufa da gyara tare da alkawarin kammala aikin a ranar 27 ga watan Mayu.

Sai dai kamfanin na daf da kammala aikin sai turken wuta daya ya kara lalacewa wanda ya dauki kwanaki kafin sanar da kammala shi a yau.

Kara karanta wannan

Kaduna: An shiga tashin hankali, wata amarya ta datse mazakutar angonta

TCN ya mika godiya ga al'umma

Kamfanin ya mika godiya ta musamman ga gwamnonin yankin Arewa maso gabas bisa hadin kai da suka bayar wajen gyaran.

Har ila yau, ya mika godiya ga al'ummar yankin bisa hakuri da suka nuna na tsawon lokacin da aka yi yayin da ake zaune a duhu.

Legit ta tattauna da Ahmad Murtala

Wani mazaunin unguwar Jekadafari da ke fadar jihar Gombe ya tabbatar wa Legit cewa sun ga canji dangane da yadda suke samun wuta bayan gyaran.

Ahmad Murtala ya ce a yankin da yake suna samun wuta sama da awa 20 bayan sanar da kammala gyaran wanda a baya ba haka bane.

An yi gyaran wutar lantarki a Abuja

A wani rahoton, kun ji cewa kamfanin rarraba wutar lantarki na Najeriya (TCN) ya sanar da cewa wasu sassa a Abuja sun shafe awanni bakwai ba tare da wuta ba.

Kara karanta wannan

Kungiyar ƙwadago ta janye yajin aiki, ta ba gwamnatin tarayya wa'adin mako 1

A cewar wata sanarwa daga TCN, ya gudanar da aiki kan wasu manyan na'urorin rarraba wutar lantarki a birnin kuma saboda haka ne ya dauke wutar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng