Gwamna Uba Sani Ya Ba da Umurni da Aka Kammala Daukar Mahajjata 4000 a Kaduna

Gwamna Uba Sani Ya Ba da Umurni da Aka Kammala Daukar Mahajjata 4000 a Kaduna

  • Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da kammala daukar mahajjatan jihar zuwa kasa mai tsarki a jiya Litinin, 3 ga watan Yuni
  • Kimanin mahajjata 4,000 ne suka tashi daga jihar Kaduna zuwa kasa mai tsarki domin gudanar da ibadar Hajji a shekarar 2024
  • Gwaman jihar, Uba Sani da sauran jami'an hukumar alhazai ta jihar sun ja hankalin mahajjatan domin ganin sun samu nasara

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna - Gwamantin jihar Kaduna ta sanar da kammala jigilar mahajjatan jihar zuwa kasa mai tsarki.

A jiya Litinin, 3 ga watan Yuni ne aka ɗauki rukunin karshe na mahajjatan su 300 zuwa kasar Saudiyya.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Gombe za ta yi titin da kilomita 1 zai lakume sama da Naira biliyan 1

Mahajjtan Kaduna
Mahajjata 4,000 sun tashi daga Kaduna zuwa Makka. Hoto: Kaduna State Pilgrims Agency
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Amirul Hajji na jihar kuma Sarkin Lere, Mai martaba Sulaiman Umar ne ya jagoranci tawagar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sakon gwamnan Kaduna ga jami'an Hajji

A lokacin da ake bankwana da alhazan, gwamnan jihar wanda Amirul Hajji ya wakilta, ya ce ya kamata jami'an hukumar alhazai su tabbatar da mutanen Kaduna sun samu kulawa.

Ya ce kamar yadda aka tanadar musu da wuraren zama masu kyau, ya kamata sauran abubuwan su tafi lafiya ta inda ba za su ji kamar sun kashe kudinsu a banza ba.

Nasihar Amirul Hajji ga mahajjatan Kaduna

Amirul Hajji na jihar, Mai martaba Sulaiman Umar ya ce ya kamata mahajjatan su san cewa za su tafi ibada ne.

Saboda haka su tabbatar sun yi komai cikin koyarwar addini kuma su yi biyayya ga malamai masu wa'azi da sauran jami'an gwamnati.

Kara karanta wannan

Gwamna ya cika alkawarin da ya ɗaukarwa alhazai 1,332, sun tashi zuwa Madinah

Bayanin shugaban hukumar mahajjata

Shugaban hukumar alhazai ta jihar, Malam Salisu S. Abubakar ya yi godiya ga daukacin wadanda suka taimaka wajen ganin jigilar mahajjatan ta tafi cikin nasara.

Ya kara da godiya ga mahajjatan kan hadin kai da su ka ba gwamnatin da ma'aikatan jirgin sama wajen bin ka'idoji da aka gindaya musu.

Mahajjata sun samu tallafi a Gombe

A wani rahoton, kun ji cewa gwamna Inuwa Yahaya ya amince a ba kowane mahajjaci tallafin N500,000 sakamakon ƙarin kuɗin hajjin 2024.

Mai magana da yawun gwamnan, Ismaila Uba Misilli, ya ce wannan matakin zai taimaka wajen ragewa alhazan raɗaɗin matsin tattalin arziki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng