Gwamnatin Gombe Za Ta Yi Titin da Duk Kilomita 1 Zai Lakume Sama da Naira Biliyan 1

Gwamnatin Gombe Za Ta Yi Titin da Duk Kilomita 1 Zai Lakume Sama da Naira Biliyan 1

  • Gwamnatin Gombe ta sanar da fara ayyukan tituna masu tsawon kilomita 18.5 a kwaryar jihar da za su lakume bilyoyi
  • Gwamna jihar Gombe, Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya ya ce ya kammala ware Naira biliyan 20 domin yin titunan
  • Legit ta tattauna da Ibrahim Sale Aliyu domin jin yadda biyunta hanyar FTH zuwa FCE(T) za ta amfani al'ummar jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Gombe- Gwamnatin jihar Gombe ta shirya kashe zunzurutun kudi sama da naira biliyan 20 domin yin tituna a jihar.

Kwamishinan ayyuka na jihar, Maijama’a Kallamu ne ya bayyana haka ga manema labarai bayan kammala zaman majalisar jihar.

Kara karanta wannan

Raya karkara: Gwamnatin Kano za ta kashe N2.6bn a gina titi mai nisan 14.7km

Gwamnan Gombe
Gwamnati za ta kashe N20b kan tituna a Gombe. Hoto: Isma'ila Uba Misilli.
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewar bayan ayyukan titunan kwamishinan ya ce gwamnan zai sayar da taki a farashi mai rahusa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Titin FTH zuwa FCE (T) Gombe

Daga cikin titunan da aikin zai shafa akwai titin da ke kan hanyar asibitin koyarwa na tarayya (FTH) zuwa kolejin ilimi da fasaha da ke Gombe.

Gwamnatin jihar ta ce za a biyunta titin ne saboda yawan cunkoso da yake haifarwa ga abubuwan hawa.

Gyaran titin Dukku zuwa Dokoro

Har ila yau gwamnatin za ta kashe Naira biliyan 1.5 a gyaran titin Dukku zuwa Dokoro da ke karamar hukumar Dukku.

Kwamishinan ayyuka na jihar ya shaida cewa za a gyara magudanar ruwa shida da ruwan sama ya lalata a kan hanyar.

Gwamnan Gombe zai samar da taki

Gwamnan jihar ya bayyana cewa zai samar da taki ga manoma a farashi mai rahusa domin bunkasa noma.

Kara karanta wannan

El-Rufai: Dan Majalisa ya bayyana yadda tsohon gwamna ya bar Kaduna cikin matsala

Cikin sakon da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Isma'ila Uba Misilli ya wallafa a shafin sa na Facebook ya nuna cewa za a sayar da buhun taki ne a N22,000 yayin da farashin kasuwa ya ke a N45,000.

Legit ta tattauna Ibrahim Sale Aliyu

Wani mazaunin jihar Gombe, Ibrahim Sale Aliyu zantawa Legit cewa biyunta hanyar FCE (T) zuwa FTH ba abu ne mai muhimmanci ba ga jihar.

Ya ce kamata ya yi gwamnatin ta yi amfani da kudin wajen biyunta hanyoyin da ake samun cinkoso a jihar sosai, kamar hanyar kasuwar Pantami.

Mahajjata sun yi zanga zanga a Makka

A wani rahoton, kun ji cewa masu mahajjatan Najeriya sun gudanar da zanga-zanga a Saudiyya biyo bayan samun matsala da aka yi kan guzurinsu.

Mahajjatan da suka taso daga Abuja sun ce hukumomi sun rage musu kuɗin guzurin da suka musu alƙawari za su ba su idan sun isa Makka.

Kara karanta wannan

Shugaban majalisa ya fadi muguwar illar da bukatar NLC za ta yiwa ma'aikata

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng