Mafi Karancin Albashi: Jagora a APC Ya Fadi Abinda Ya Kamata a Biya Ma'aikata

Mafi Karancin Albashi: Jagora a APC Ya Fadi Abinda Ya Kamata a Biya Ma'aikata

  • Daniel Bwala ya fadi ra'ayinsa dangane da taƙaddamar da ake yi kan mafi ƙarancin albashin ma'aikata tsakanin gwamnatin tarayya da ƴan ƙwadago
  • Ya bayyana cewa kamata ya yi gwamnati ta biya ma'aikatan Najeriya mafi ƙarancin albashin da ya kai N250,000
  • Ya yi nuni da cewa N60,000 da gwamnati ta tayin za ta biya a matsayin mafi ƙarancin albashi ya yi kaɗan duba da yadda rayuwa ta yi tsada a ƙasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Na kusa da shugaban ƙasa, Bola Tinubu, Daniel Bwala, ya bayyana mafi ƙarancin albashin da ya kamata gwamnati ta biya ma'aikata.

Daniel Bwala ya bayyana cewa kamata ya yi mafi ƙarancin albashin ma'aikatan Najeriya ya kasance N250,000.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya shiga muhimmin taro kan mafi karancin albashi, bayanai sun fito

Bwala ya yi magana kan mafi karancin albashi
Daniel Bwala ya fadi mafi karancin albashin da ya dace gwamnati ta biya Hoto: @DOlusegun, @BwalaDaniel
Asali: Twitter

Ma'aikata sun shiga yajin aiki kan albashi

Daniel Bwala ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da tashar TVC News kan yajin aikin da ƙungiyoyin ƙwadago suka fara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƙungiyoyin ƙwadagon sun shiga yajin aiki ne kan sabon mafi ƙarancin albashi da ƙarin kuɗin wutar lantarki ga masu amfani da rukunin 'Band A'.

A daren ranar Litinin, 3 ga watan Yunin 2024, gwamnatin tarayya da ƙungiyoyin ƙwadago sun cimma yarjejeniya kan sabon mafi ƙarancin albashi wanda zai wuce N60,000.

Me Bwala ya ce kan ƙarin albashi?

Daniel Bwala ya bayyana cewa N60,000 da gwamnati ta yi tayin za ta biya a matsayin mafi ƙarancin albashi ya yi kaɗan.

"Duba da hauhawar farashin kayan abinci da tsadar rayuwa a Najeriya, N60,000 ba za ta je ko'ina ba."
"Ko gwamnatin tarayya ta san da hakan. Ban tunanin duk wani mai cikakken hankali zai ce abin da ƴan ƙwadagon ke neman shirme ne. A'a abu ne da ya cancanta amma ba za a iya samar da shi ba."

Kara karanta wannan

Yajin aiki: Abubuwan da aka Amince da su a taron Gwamnatin Tinubu da ƴan ƙwadago

"Ina tunanin ya kamata gwamnati ta ƙara abin da ta ce za ta biya. Ban tunanin gwamnati na cewa N60,000 shi ne ƙarshen abin da za ta iya biya."
"Idan aka tambayeni, a tunanina kamata ya yi mafi ƙarancin albashi ya kasance N250,000 a Najeriya. Amma idan kana tunanin haka ya dace amma ba kuɗin da za a iya biya, sai a yi haƙuri da abin da ya samu."

- Daniel Bwala

NLC ta janye yajin aikin ma'aikata

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyoyin ƙwadagon Najeriya na NLC da TUC sun dakatar da yajin aikin sai baba ta gani da suka fara a ranar Litinin a faɗin ƙasar nan.

NLC da TUC sun tsagaita yajin aikin ne na mako ɗaya rak, a kokarin da suke yi na ganin su da gwamnatin tarayya an cimma matsaya kan mafi ƙarancin albashi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel