Kano: Fitaccen Basarake Ya Magantu Kan Dawo da Sanusi II, Ya Tura Masa Sako Na Musamman
- Sarki Muhammadu Sanusi II yana ci gaba karbar sakwannin taya murna daga manyan sarakuna da ƴan siyasa
- Sarkin Gwandu a jihar Kebbi, Manjo-janar Muhammad Ilyasu Bashir shi ma ya taya Sarkin murnan dawowa kujerar sarautar Kano
- Sarkin ya ce tabbas wannan nadin ya yi dai-dai duba da kwarewa da kuma jajircewa irin na Muhammadu Sanusi II
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kebbi - Sarkin Gwandu a jihar Kebbi, Manjo-janar Muhammad Ilyasu Bashir mai ya taya Sarki Muhammadu Sanusi II murna.
Ilyasu Bashir ya tura sakon murnan ne ga Sanusi II bayan dawowa kan kujerar sarautar Kano a kwanakin baya.
Sarkin Gwandu ya taya Sanusi II murna
Mai Martaba ya ce wannan ba karamin ci gaba ba ne duba da kwarewar Sarki Muhammadu Sanusi II, cewar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sarkin ya kuma roki Allah ya ba Sanusi II hikima da kwazo wurin gudanar da shugabanci ba tare da nuna wariya ba.
Har ila yau, sarkin ya bukaci al'umma da su zauna lafiya da juna yayin da ake rigimar sarauta a jihar.
Gwamna ya ji dadin maido Muhammadu Sanusi II
Har ila yau, Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers ya fara taya Sarki Muhammadu Sanusi II murnar dawowa kujerar sarautar Kano.
Fubara ya bayyana jin dadinsa kan wannan mataki na Gwamna Abba Kabir inda ya ce tabbas hakan zai kawo ci gaba a jihar ganin yadda al'umma ke goyon bayan matakin.
Gwamnan ya bayyana haka a ranar Alhamis 23 ga watan Mayu yayin da suke gudanar da wani babban taro a jihar tare da Sanusi II a birnin Port Harcourt da ke jihar Rivers.
Ƴaƴan Dahiru Bauchi sun ziyarci Sanusi II
A wani labarin, kun ji cewa ƴaƴan Sheikh Dahiru Bauchi sun kawo ziyara fadar Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II a ranar Litinin.
Tawagar karkashin jagorancin Aminu Dahiru Bauchi ta kai ziyarar domin nuna goyon baya ga Sarkin tare da nuna jin dadinsu.
Wannan na zuwa ne bayan tube sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero tare da mayar da Muhammadu Sanusi II kujerar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng