Rigimar Sarautar Kano: Sanusi II Ya Samu Goyon Bayan Kungiyar Lauyoyin Najeriya

Rigimar Sarautar Kano: Sanusi II Ya Samu Goyon Bayan Kungiyar Lauyoyin Najeriya

  • Kungiyar lauyoyin Najeriya (NBA) ta gayyaci Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II zuwa wani babban taro da ta gudanar a jihar
  • A yayin da ake ci gaba da fafata rikicin sarautar Kano, NBA ta amince da Sanusi II a matsayin halattaccen sarkin masarautar
  • Sarkin Kano Sanusi II wanda ya yi jawabi a taron ya ce har sai akwai karfin shari'a a ƙasa ne al'uma ke iya yin rayuwa cikin salama

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Kano - A yayin da ake ci gaba da fafata rikicin sarautar Kano, kungiyar lauyoyin Najeriya (NBA) ta amince da Muhammadu Sanusi II a matsayin halaltaccen sarkin masarautar.

Kara karanta wannan

Kano: Abin da ƴaƴan Sheikh Dahiru Bauchi suka faɗawa Sanusi II bayan kai masa ziyara

Kungiyar lauyoyin Najeriya ta yi magana kan rigimar masarautar Kano
Kungiyar lauyoyin Najeriya sun yi mubayi'a ga Sanusi II a matsayin sarkin Kano. Hoto: @masarautarkano
Asali: Twitter

Wannan na zuwa bayan da shugabannin kananan hukumomi 44 na Kano da hakimansu, kwamishinoni da wasu manyan jihar suka yi mubaya'a ga sabon sarkin.

Kungiyar NBA ta gayyaci Sanusi II taro

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa an fahimci kungiyar NBA ta amince da nadin Sanusi II ne bayan ta gayyace shi taronta na shekara da ke gudana yanzu a Kano.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

La'akari da girman wannan taron, kungiyar lauyoyin ta gayyaci Sarki Sanusi II domin ya gabatar da jawabin sanya albarka a matsayinsa na uban ƙasa.

An ce kungiyar ta NBA ba ta gayyaci Alhaji Aminu Ado Bayero ba, wanda dokar masarautar Kano ta 2024 ta kore shi daga karagar mulki a matsayin Sarkin Kano na 15.

Sarki Sanusi II ya yi magana kan shari'a

A jiya Litinin ne babbar kotun tarayya da ke Kano ta shirya sauraron karar da aka shigar gabanta kan rigimar masarautar amma saboda yajin aikin NLC ba ta samu zama ba.

Kara karanta wannan

"Ka dauki kaddara": An taso Sarkin Kano Sanusi II a gaba kan hudubar sallar Juma'a

Sarki Sanusi II wanda ya yi jawabi a taron kungiyar NBA ta bakin wakilinsa, Mahe Bashir Wali (Walin Kano) ya yiwa baki maraba da nuna girman al'adun jihar Kano.

Sarkin ya ce har sai akwai karfin shari'a a ƙasa ne al'uma ke iya yin rayuwa cikin salama, wanda kuma ya ce bunkasar al'uma na tattare da karfin shari'a, in ji rahoton Independent.

Gwamnan Kano ya ƙalubalanci lauyoyi

A bangaren gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf kuwa, ya yi amfani da damar wajen ƙalubalantar NBA kan makomar umarnin kotuna biyu game da rigimar masarautar jihar.

Gwamnan wanda ya samu wakilcin sakataren gwamnatin jihar, Abdullahi Bappa Bichi ya nemi lauyoyin da suka rika wayar da kan abokan huldarsu kan hurumin kotuna a shari'a.

Abba Yusuf ya ce akwai kotun da ba ta da hurumin sauraron shari'ar rigimar masarautar Kano kasancewar rigima ce ta cikin gida, da kotun jiha ke da hurumin saurare.

Kara karanta wannan

Sarautar Kano: Abin da Sarki Sanusi II ya gargadi hakimai da ciyamomi 44 a kai a fadarsa

Sarki Sanusi II ne Sarkin Kano - NBA

Da yake zantawa da manema labarai kan rikicin masarautar Kano, Barista O.M Femi ya ce kungiyar NBA ba ta da masaniya kan abin da ke faruwa.

Barista O.M Femi ya ce:

“Duk da haka, ba ka bukatar a gaya maka ko ka sanya tabarau kafin ka san cewa Mai Martaba Muhammadu Sanusi II ne Sarkin Kano a yanzu.

"Haka zalika, gayyatar Sarki Sanusi II zuwa wannan babban taron na NBA zai kara ba ka tabbaci na wanda muke kallo a matsayin Sarkin Kano.

An soki hudubar Juma'ar Sarki Sanusi II

A wani labarin, mun ruwaito cewa hudubar sallar Juma'a da Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya gabatar a babban masallaci ta jawo ce-ce-ku-ce.

Yayin da wasu ke zargin sarkin da yin amfani da mumbari da nassi wajen yin habaice-habaice, wasu kuma sun yi ikirarin cewa Sarki Sanusi II na tallata manufofinsa ne a fili.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel