Yan Bindiga Sun Farmaki GRA Katsina, Sun Sace Farfesa da Wani Lakcara a Jami'ar Tarayya

Yan Bindiga Sun Farmaki GRA Katsina, Sun Sace Farfesa da Wani Lakcara a Jami'ar Tarayya

  • Wasu lakcarori biyu a Jami'ar Tarayya a Dutsinma sun gamu da iftila'i bayan ƴan bindiga sun yi awon gaba da su a jihar Katsina
  • Lamarin ya faru ne da safiyar jiya Litinin 3 ga watan Yuni a karamar hukumar Dutsinma da ke jihar a Arewacin Najeriya
  • Wadanda abin ya shafa sun hada da Farfesa Richard Kyaram da kuma ɗansa mai suna Solomon da wani Dakta Hamza

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Katsina - Ƴan bindiga sun yi garkuwa da lakcarori a Jami'ar Tarayya da ke Duntsinma a jihar Katsina.

Miyagun sun sace lakcarori biyu tare da wani mutum guda da safiyar ranar Litinin 3 ga watan Yuni a jihar.

Kara karanta wannan

Yajin Aiki: Ma'aikatan gwamnati a jihar Kano sun bi umarnin kungiyoyin NLC da TUC

Yan bindiga sun sace lakcarori 2 a jihar Katsina
Yan bindiga sun sace lakcarori 2 a Jami'ar Tarayya da ke Duntsinma a jihar Katsina.
Asali: Original

Katsina: 'Yan bindiga sun sace lakcarori 2

The Guardian ta tattaro cewa maharan sun sace Farfesa Richard Kyaram da ɗansa mai suna Solomon da kuma wani Dakta Hamza.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wadanda aka sacen suna rayuwa ne a yankin GRA da ke Dutsinma inda maharan suka farmaki yankin da muggan makamai.

Wata majiya ta tabbatar da cewa maharan sun bi gida-gida inda suke kwacen waya da kudi da sauran kayayyaki masu amfani.

"Daga bisani an fitar da wadanda aka sacen daga gidajensu inda aka tafi da su wani wuri da ba a sani ba."

- Majiyar

Wane martani ƴan sanda suka yi?

Kakakin rundunar ƴan sanda a jihar Katsina, ASP Abubakar Aliyu bai yi martani kan lamarin ba da ƴan jaridu suka tuntube shi.

Har ila yau, mai magana da yawun Jami'ar, Habibu Umar shi ma bai ce komai har zuwa lokacin tattara wannan rahoto.

Kara karanta wannan

Dambarwar sarauta: Kanawa sun nemi taimakon Abba, ƴan daba sun mamaye Kano

Ƴan bindiga sun hallaka mutane a Katsina

A wani labarin, kun ji cewa 'yan bindiga sun hallaka aƙalla mutum 17 a wasu hare-hare da suka kai a wasu ƙauyukan jihar Katsina.

Harin baya-bayan nan ya auku ne a ranar Alhamis lokacin da ƴan bindigan suka farmaki wata motar haya a kusa da Dan Marke a kan hanyar Kankara zuwa Marabar Kankara.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.