CBN Zai Kwace Lasisin Keystone da Wasu Bakuna 2? Babban Bankin Ya Fitar da Bayani
- Rahotannin da ke yawo a yanar gizo kan cewa bankin CBN zai soke lasisin bankunan Unity, Polaris, da Keystone ba gaskiya ba ne
- Babban bankin Najeriya ya fito ya karyata wannan labarin a yau Talata, 4 ga watan Yuni, abin da ya jawo mutane yin ce-ce-ku-ce
- A jiya Litinin ne bankin CBN ya sanar da kwace lasisin bankin Heritage saboda ya saɓa sashe na 12 (1) na dokar BOFIA ta shekarar 2020
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Babban bankin Najeriya (CBN) ya ce ba shi da wani shiri na kwace lasisin bankunan Unity, Polaris da kuma Keystone.
Rahotanni na yanar gizo sun yi ikirarin cewa babban bankin zai soke lasisin bankunan uku, biyo bayan soke lasisin bankin Heritage.
Sai dai a wani rubutu da bankin ya wallafa a shafinsa na X a ranar Talata, ya ce rahoton da ke ake yadawa ba sahihai ba ne.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Asalin labarin karbe lasisin bankuna
A jiya Litinin, 3 ga watan Yuni, shafin yanar gizo na The Scrutiny ya wallafa cewa CBN ya shirya dakatar da lasisin wasu bankuna guda uku,.
Bankunan uku da abin ya shafa su ne Unity, Keystone da Polaris, "wata majiya mai tushe a babban bankin ta sanar da TheScrutinyNG".
Rahoton ya yi ikirarin cewa:
"Bankunan da abin ya shafa sun dade suna fama da matsalar kudi, kuma CBN ba ta da wani zabi da ya wuce ta dakatarsu saboda gudun lalata tsarin hada-hadar kudi".
CBN zai kwace lasisin bankunan?
Amma a martanin da babban bankin kasar ya fitar a safiyar yau Talata, 4 ga watan Yuni, ya ce:
"Abin da ake yadawa karya ne, ba daga CBN ya fito ba."
Jim labarin cewa CBN zai kwace lasisin bankunan ya jefa 'yan Najeriya musamman abokan huldarsu shiga damuwa, inda wasu suka fara kokarin kwashe kudaden su.
'Yan Najeriya sun magantu
Ma'abota amfani da soshiyal midiya sun magantu kan labarin karya na cewa CBN zai kwace lasisin bankunan Unity, Polaris da Keystone.
@olumidecapital:
"Wannan ba abin wasa ba ne, hakan ya jawo barna sosai ga masu zuba jari a bankunan a jiya."
@oshinterbz:
"Ni da har na riga da na rufe asusun banki na keystone a jiyan"
@luxlyangels:
"Ya kamata a garkame mawallafin jaridar. Yanzu lokacin da ya kamata a saka dokar amfani da soshiyal midiya ko jama'a za su koyi darasi."
CBN ya kwace lasisin bankin Heritage
A ranar 4 ga watan Yuni muka ruwaito cewa babban bankin Najeriya (CBN) ya kwace lasisin bankin Heritage bayan ya saɓa sashe na 12 (1) na dokar BOFIA 2020
A cewar CBN, an yanke hukuncin ne saboda gazawar bankin na inganta ayyukansa na hada-hadar kudi duk da tarin uzuri da babban bankin ya yi masa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng