CBN ta kwace lasisin kamfanonin hada-hadar kudi 182 a Najeriya

CBN ta kwace lasisin kamfanonin hada-hadar kudi 182 a Najeriya

Babban Bankin Najeriya CBN ta bayar da sanarwar janye lasisin aiki na wasu bankuna da kamfanonin hada-hadar kudade guda 182.

Wannan sanarwan na zuwa ne makonni kadan bayan babban bankin ta kwace lasisin Skye Bank tare da bayar da umurnin wata bankin da karbe abokan huldan tsohuwar bankin.

A cewar sanarwar da CBN ta saka a shafinta na yanan gizo, bankuna da za'a karbe lasisin na su sun hada da Bankunan Bayar da Kananan Basusuka 154, Bankunan Bayar da Bashin Gidaje 6 da kuma wasu kamfanonin hada-hadan kudi 22.

CBN ta kwace lasisin kamfanonin hada-hadar kudi 182 a Najeriya
CBN ta kwace lasisin kamfanonin hada-hadar kudi 182 a Najeriya
Asali: Getty Images

DUBA WANNAN: Yaki da rashawa: Magu ya yiwa 'barayin gwamnati' sabuwar albishir

Sanarwan ta ce Bankunan Bayar da Kananan Basusuka 62 tuni sun rufe, wasu 74 kuma ba su iya tafiyar da harkokinsu, yayin da 12 daga cikinsu suna fama da manyan matsaloli su kuma sauran shida na karshe sun rufe.

Ahocol Savings Limited, mallakar gwamnatin jihar Anambra ta rufe, yayin da Trans Atlantic Savungs and Loans Limited mallakar gwamnatin Jihar Bayelsa ta dena aiki domin bashi ya yi mata katutu.

Alkalluman CBN ta fitar ya nuna cewa an yiwa Bankunan Bayar da Kananan Basusuka 1028 rajista fara aiki a Najeriya amma cikinsu 20 ne kawai suka sabunta lasisin aikinsu da babban bankin na kasa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel