Da dumin sa: Babban bankin Najeriya ya kwace lasisin bankuna 9 a Arewa

Da dumin sa: Babban bankin Najeriya ya kwace lasisin bankuna 9 a Arewa

Babban bankin Najeriya dake da alhakin tafiyar da tattalin arzikin kasa mun samu cewa ya kwace lasisin gudanarwa na kananun bankuna 9 cikin 32 habaka tattalin arziki watau micro finance banks a jihar Neja dake a Arewa ta tsakiyar Najeriya.

Babban Sakataren kungiyar ma'aikatan kananan bankunan ne dai na shiyyar Arewa ta Tsakiya Mista Sado Daniel ya shaida wa wakilin majiyar mu hakan a garin Bida inda yaje bude wani karin karamin bankin.

Da dumin sa: Babban bankin Najeriya ya kwace lasisin bankuna 9 a Arewa
Da dumin sa: Babban bankin Najeriya ya kwace lasisin bankuna 9 a Arewa
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Neman Janar Alkali: Sojoji sun fitar da sabuwar sanarwa

Legit.ng Hausa ta samu cewa da yake tsokaci game da dalilin kwace lasisin gudanarwar na bankunan, Mista Daniel ya bayyana cewa rashin gaskiya da kuma kwarewa ce ainihin musabbabin durkushewar bankunan.

Idan mai karatu bai manta ba dai a farkon watan nan ne babban bankin na Najeriya ya kwace bankin Sky saboda yawan bashin dake kan sa ya kuma ceto shi daga durkushewa kafin daga bisani ya mika shi ga wani sabon bankin mai suna Polaris.

A wani labarin kuma, gwamnan jihar Benue dake a shiyyar Arewa ta tsakiya, Samuel Ortom ya bayyana babban dalilin da ya sa shi da jama'ar jihar sa mafi yawa daga cikin su ba su kaunar shugaban kasa, Muhammadu Buhari kuma basu son ya zarce a 2019.

Gwamnan wanda ya ce ko kusa ba wai don shugaban kasar yana dan kabilar fulani bane, domin a cewar sa, 'yan jihar tasa suna zaune lafiya da duk fulanin dake zagaye da su shekaru aru-aru da suka gabata.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng