CBN ya kwace lasisin bankin Skye Nigeria Plc, kwastomomi zasu koma wani sabon banki

CBN ya kwace lasisin bankin Skye Nigeria Plc, kwastomomi zasu koma wani sabon banki

- CBN ya kwace lasisin gudanar da aiki na bankin Skye Plc

- Babban bankin ya yanke hukuncin kafa wani sabon banki da sunan 'Polaris Bank', don zama madadin bankin Skye

- Sabon bankin zai fara aiki a ranar Litinin, 24 ga watan Satumba, 2028

Babban bankin Nigeria CBN ya kwace lasisin gudanar da aiki na bankin Skye Plc bayan da ta shafe shekaru biyu tana dagawa bankin kada akan wasu dalilai.

Gwamnan CBN, Godwin Emefiele a lokacin da ya ke ganawa da manema labarai a Legas, ya ce: "A matsayinmu na hukumar gudanarwar bankuna, kuma wadanda ba sa yanke hukunci sai sun tuntubi hukumar inshoran masu ajiye kudade ta kasa NDIC, zuwa yanzu mun yanke hukuncin kafa wani sabon banki da sunan 'Polaris Bank', don kwashe komai na bankin Skye."

Ya ce: "Bayan gudanar da bincike musamman akan gudanarwar ayyukan bankin, mun sanar da cewa bankin Skye na bukatar kudade masu yawa idan har yana son ci gaba da aiki da kuma samun rance daga babban bankin kasa. Amma masu saka hannun jari a bankin sun kasa samar da wadannan kudade."

KARANTA WANNAN: Karshen alewa: Rundunar yan sanda ta cafke wanda ya kashe Farfesan jami'ar Kashere

CBN ya kwace lasisin bankin Skye Nigeria Plc, kwastomomi zasu koma wani sabon banki
CBN ya kwace lasisin bankin Skye Nigeria Plc, kwastomomi zasu koma wani sabon banki
Asali: Getty Images

Idan za a iya tunawa a ranar 4 ga watan Yulin 2016, CBN ya dauki wani mataki akan bankin Skye Nigeria Plc, wanda ya zama silar murabus din shugaban bankin, da dukkanin kananan daraktoci gami da manajan darakta tare da mataimakinsa, da kuma wasu manyan daraktoci guda biyu da suka dade a hukumar gudanarwar bankin.

A hukuncin da CBN ya yanke yanzu, ana sa ran kamfanin da ke kula da harkokin kadarori na kasa AMCON zai samarwa bankin na Skye kudaden gudanarwa, tare da nemo masu saka hannun jari da za su sayi kadarorin AMCON.

Emefiele ya ce: "Don haka muke tabbatarwa wadanda suka ajiye kudinsu a bankin, da su kwantar da hankulansu, domin kidadensu na nan kuma hada-hadarsu za ta ci gaba a sabon bankin zuwa ranar Litinin, 24 ga watan Satumba, 2028, don baiwa kwastomomi damar yin amfani da kudaden da suka ajiye a bankin."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel