"Mafita 1 Ta Rage," Babban Malamin Addini Ya Taɓo Ciwon da Ya Fi Damun Ƴan Najeriya

"Mafita 1 Ta Rage," Babban Malamin Addini Ya Taɓo Ciwon da Ya Fi Damun Ƴan Najeriya

  • Babban limamin cocin RCCG, Fasto Enoch Adejare Adeboye, ya koka kan halin ƙunci da wahalar rayuwar da ƴan Najeriya suka tsinci kansu
  • Ya ce halin da kasar nan ke ciki abin kyama ne kuma mutane da yawa ba za su iya jurewa ba yayin da yajin aikin NLC ya kankama
  • Ya roƙi ƴan Najeriya su tashi tsaye su dage da addu'ar Allah ya kawo sauƙi domin shi ne kaɗai wanda zai iya yaye wannan halin da aka shiga

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Babban malamin cocin RCCG a Najeriya, Fasto Enoch Adejare Adeboye ya fahimci halin ƙunci da wahalhalun da galibin ƴan Najeriya ke fuskanta a ƙasar nan.

Ya bayyana cewa mafi akasarin ƴan Najeriya ba za su iya jure wahalar da ake ciki a wannan karon ba.

Kara karanta wannan

"Ba addu'a ba ce": Malamin addini ya fadi abin da zai sa a samu sauki a Najeriya

Fasto Adeboye na cocin RCCG.
Malamin coci ya ja hankalin ƴan Najeriya kan su miƙa lamarinsu ga Allah Hoto: RCCOG
Asali: Facebook

Fasto ya ce ana cin kwakwa a Najeriya

Fasto Adeboye ya roki ‘yan Najeriya da su roki Allah Madaukakin Sarki domin ya kawo masu ɗauki, inda ya ce ya aminta cewa halin da kasar ke ciki ya gajiyar da mutane da dama.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar Telegraph ta ce malamin cocin ya yi wannan tsokaci mai ratsa zuciya ne a lokacin da yake jawabi a taron wa'azin shigowar watan Yuni mai taken “daga kai na."

Taron wa'azin da aka gudanar a hedkwatar cocin na kasa (TOG) Ebute-Metta, ya samu halartar mutane daga ɓangarori daban-daban.

Adeboye ya faɗi mafita 1 ga jama'a

Faston ya yiwa mutane nasiha cewa a duk lokacin da aka shiga wani yanayi da ya fi ƙarfin ɗan Adam, abu na gaba shi ne neman taimakon Ubangiji.

"Idan kuna buƙatar agaji, idan gari ya yi zafi kuma ni na san da yawan mu suna cikin wahala, ku kira wanda ke da iko a kan komai, Allah wanda zai iya magance kamai."

Kara karanta wannan

InnaliLahi: Mutane 30 sun mutu a wani mummunan ibtila'i da ya rutsa a Arewa

Ya ƙara da cewa babu wani abu da ba zai yiwu ba a wurin Allah, don haka ya kamata mutane su koma gare Shi idan suka rasa mafita.

Gwamnati ta gana da NLC da TUC

A wani labarin kuma wakilan gwamnatin tarayya da ƴan kwadago sun fito daga taron gaggawa da aka shirya kan mafi ƙarancin albashin ma'aikata a Najeriya

NLC da TUC sun tsunduma yajin aiki bayan gaza cimma matsaya da gwamnatin tarayya a taron da aka yi ranar 31 ga watan Mayu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262