Hajji: Mahajjata Sun Kunyata Mahukuntan Najeriya, Sun Yi Zanga Zanga a Saudiyya

Hajji: Mahajjata Sun Kunyata Mahukuntan Najeriya, Sun Yi Zanga Zanga a Saudiyya

  • Rahotanni da ke fitowa daga waje sun nuna cewa mahajjatan Najeriya sun yi zanga zangar lumana a kasa mai tsarki
  • Wasu daga cikin mahajjatan sun bayyana cewa zanga-zangar ta biyo bayan rashin jin dadi da ya shafi guzurinsu ne
  • Maniyyatan sun kuma bayyana yadda lamarin ya fara faruwa tun suna kokarin tashi daga Najeriya zuwa kasa mai tsarki

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Saudi Arabia: Mahajjatan Najeriya da suka fito daga birnin tarayya Abuja sun gudanar da zaga zangar lumana Makkah.

Mahajjatan sun ce an samu matsala kan kuɗaɗen guzurinsu da aka ce za a ba su idan sun isa kasa mai tsarki.

Kara karanta wannan

Masana sun fallasa yadda gwamnatin tarayya da dawo da tallafin man fetur a boye

Hajjin bana
Mahajjatan Najeriya sun yi zanga zanga saboda rage musu guzuri. Hoto: Hoto: @MoHU_En
Asali: Twitter

BBC Hausa ta ruwaito cewa mahajjatan sun zargi wasu daga cikin ma'aikata da yin ba daidai ba da kudin guzurin nasu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me ya tayar da zanga zangar Mahajjata?

Wasu daga cikin mahajjatan sun bayyana cewa tun suna gida Najeriya aka musu alkawarin kudin guzuri dala 500.

Amma sai ga shi an ba su dala 400, an zaftare musu dala 100, hakan kuma ya fusata su har suka tayar da zanga-zangar.

Meyasa aka ba Mahajatta Dala 400?

Wani mahajjaci ya tabbatar da cewa a lokacin da aka ba su dala 200 a Najeriya, an ce masu sai sun je kasa mai tsarki za a kara musu dala 300.

Hukumomin sun ce masu hakan ya faru ne saboda ƙarancin dalar Amurka a lokacin da suke ƙoƙarin tashi zuwa kasa mai tsarki.

Yadda aka yi bayan isa Saudiyya

Kara karanta wannan

Yajin Aiki: Ma'aikatan gwamnati a jihar Kano sun bi umarnin kungiyoyin NLC da TUC

Mahajjacin ya cigaba da cewa a lokacin da suka isa kasa mai tsarki sai aka ba su dala 200 maimakon dala 300 da aka yi masu alkawari.

Su kuma sai suka ga ba su da mafita sai dai su gudanar da zanga zanga domin nuna bacin rai da neman hakkinsu.

Najeriya za ta inganta lafiyar Mahajjata

A wani rahoton, kun ji cewa hukumar alhazai ta kasa ta shawarci maniyyatan Najeriya masu bukatar kulawar lafiya da su ziyarci asibitocin gwamnatin Saudiyya.

NAHCON ta ce tana jiran amincewar Saudiya domin kafa asibitocinta a Makkah, yayin da ta samu izinin yin hakan a garin Madinah.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng