N65, 000: ’Yar Kwadago Ta Fadi Albashin da Ya Kamata a Rika Biyan ’Yan Majalisun Najeriya
- Shugabar kungiyar ma'aikatan lafiya ta Najeriya, Bamgbose Betty ta yi kira da a rika biyan ‘yan majalisun Najeriya mafi karancin albashi
- Bamgbose Betty ta ce idan 'yan majalisun suka dawo karbar mafi karancin albashi hakan zai nusar da su halin da talaka yake ciki
- Shugabar kungiyar 'yan kwadagon ta kuma bayyana cewa albashin da ma'aikata ke karba a yanzu ba ya wuce kwana uku ya kare
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jihar Legas - Wata 'yar kungiyar kwadago ta NLC ta yi kira da a rika biyan ‘yan majalisun Najeriya mafi karancin albashi na Naira 65,000.
Tsohuwar ma'ajin kungiyar NLC kuma shugabar kungiyar ma'aikatan lafiya ta Najeriya, Bamgbose Betty ta ce ta yi wannan kiran a jiya Litinin a Legas.
A zantawarta da News Central TV, Bamgbose Betty, ta ce idan 'yan majalisun kasar suka dawo karbar mafi karancin albashi hakan zai koya masu darasi kan halin da talaka yake ciki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yar kwadago ta yi maganar 'yan majalisu
Shugabar kungiyar 'yan kwadagon ta kuma bayyana cewa albashin da ma'aikata ke karba a yanzu ba ya isa ya biya su bukatunsu na wata-wata ba.
Bamgbose Betty ta ce:
"Albashi ne da ka karbe shi ko kwana uku ba ya yi zai kare. Muna cikin mawuyacin hali yayin da gwamnati ke ta faman zaman tattaunawa ba tare da an cimma wata matsaya ba.
"Idan har suna son sanin gaskiyar halin da talaka yake ciki, to ya kamata 'yan majalisun su dora kansu a tsarin mafi karancin albashi da ake biyan ma'aikata."
Ta ci gaba da cewa, tunda ‘yan majalisun Najeriya sun ki fahimtar halin da karamin ma'aikaci yake ciki kuma sun ki taimakawa ya samu sauki, to ya kamata a sanya su albashi daya.
Kalli bidiyon a kasa:
'Yan kwadago sun rufe ofishin ministan Abuja
A wani labarin, mun ruwaito cewa 'yan kwadago sun rufe ginin ma'aikatar babban birnin tarayya Abuja inda ofishin Minista Nyesome Wike ya ke.
'Yan kwadagon sun dura ginin ma'aikatar ne tare da hana shiga ko fita domin tabbatar da bin umarnin kungiyoyin kwadago na kasa na shiga yajin aikin gama gari.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng