"Na Koyi Darasi": Obasanjo Ya Fadi Yadda Ya Ƙi Amincewa da Taimakon Tsohon Sarki a Gidan Kaso
- Tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo ya tuna alherin da marigayi Lamidon Adamawa ya yi masa a gidan yari
- Obasanjo ya bayyana yadda rayuwar gidan yari ta zama alheri a gare shi wurin ba shi damar inganta Najeriya bayan zama shugaban ƙasa
- Wannan na zuwa ne bayan Obasanjo ya je birnin Yola na jihar Adamawa domin ƙaddamar da aiki a jiya Litinin 3 ga watan Yuni
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Adamawa - Tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya magantu kan halin da ya shiga a gidan yari da ke garin Yola.
Obasanjo ya ce zamansa a gidan kaso ya sauya masa rayuwa tare da tasiri wurin inganta Najeriya bayan ya zama shugaban kasa.
Obasanjo ya fadi alherin zaman gidan yari
Tsohon shugaban ya bayyana haka ne a jiya Litinin 3 ga watan Yuni a Yola yayin kaddamar da wani aiki na Gwamna Ahmadu Fintiri a cewar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce zama a gidan kaso a Yola ya zama masa alheri a rayuwarsa musamman bayan kasancewa shugaban kasa., ThisDay ta tattaro wannan.
Yadda tsohon Sarki ya taimaki Obasanjo
"Lokacin da nake gidan yari a nan, marigayi Lamido ya dauke ni kamar ɗansa, ya tura min wani domin ba ni kyautar na'urar ba da iska (AC)."
"Na ce masa Mai Martaba wanda ya saka ni a nan bai son na ji dadi, ka bar ni kawai na yi fama da fanka."
"Na fada masa cewa ko da an saka hukumomi za su cire ba tare da bata lokaci ba."
- Olusegun Obasanjo
A martaninsa, Gwamna Ahmadu Fintiri ya godewa tsohon shugaban kasar kan yadda ya mutunta gayyatar da ya yi masa domin ƙaddamar da aikin.
Obasanjo ya bukaci ba matasa dama
Kun ji cewa tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo ya magantu kan ba matasa dama a shugabanci.
Obasanjo ya ce lokaci ya yi da ya kamata a gwada sababbin jini domin tabbatar da gudanar da shugabanci mai inganci.
Tsohon shugaban ya koka kan yadda yanzu Najeriya ta dawo ƙasa mafi hatsari da dan Adam zai yi rayuwa a ciki saboda rashin shugabanci.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng