Kano: Abin da Ƴaƴan Sheikh Dahiru Bauchi Suka Faɗawa Sanusi II Bayan Kai Masa Ziyara
- Yayin da ake ci gaba da mubaya'a ga Muhammadu Sanusi II, ƴaƴan Sheikh Dahiru Bauchi sun ziyarci Sarkin Kano a fadarsa
- Ƴaƴan babban malamin Tijjaniya sun kawo ziyara fadar Sanusi II domin nuna goyon bayan ga Sarkin inda suka bayyana jin dadinsu kan lamarin
- Wannan na zuwa ne bayan dawo da Mai Martaba Sanusi II bayan tube sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero a Kano
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Wasu daga cikin ƴaƴan Sheikh Dahiru Bauchi sun ziyarci Sarki Muhammadu Sanusi II a fadarsa da ke Kano.
Tawagar wanda Aminu Dahiru Bauchi ya jagoranta ta kai ziyarar a jiya Litinin 3 ga watan Yuni.
Kano: Sanusi II ya karbi manyan baki
Daily Nigerian ta tattaro cewa yayin ziyarar, ƴaƴan shehin malamin sun bayyana jin dadi tare da godiya ga Ubangiji bayan dawowar Sanusi II.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sun bayyana irin ci gaba da dawowar sabon sarkin zai kawo ga jihar musamman a dai-dai wannan lokaci.
"Mun zo Kano ne domin nuna goyon baya da kuma caffan ban girma ga Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II."
"Muna farin ciki da dawowar Sarki Sanusi a matsayin Sarkin Kano."
"Tabbas hakan ba karamar nasara ba ce kuma muna da tabbacin zai kawo ci gaban tattalin arziki na zamantakewar rayuwa."
- Aminu Dahiru Bauchi
Kano: Ziyarar hakimai fadar sarki Sanusi II
Wannan na zuwa ne kwanaki biyu bayan hakimai da dagatai da kuma shugabannin riko na kananan hukumomi 44 na jihar Kano sun kai caffan ban girma ga Sanusi II.
Hakiman da ciyamomin sun nuna goyon bayan tare da yin addu'o'i ga sabon Sarkin a fadarsa da ke jihar.
Kungiya ta magantu kan rushe masarautun Kano
A wani labarin, kun ji cewa Kungiyar Arewa Truth and Justice Initiative ta yi martani kan rusa masarautun jihar Kano da Gwamna Abba Kabir ya yi.
Kungiyar ta caccaki Abba Kabir kan tube sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero tare da mayar da Muhammadu Sanusi II.
Ta ce Abba Kabir ya yi hakan ne domin yin rufa-rufa kan gazawarsa game da mulkin jihar da ya yi a cikin shekara daya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng