Yajin Aikin NLC: Kungiyar MURIC ta Tona Abin da ya Faru da Jirgin Maniyyatan Aikin Hajji

Yajin Aikin NLC: Kungiyar MURIC ta Tona Abin da ya Faru da Jirgin Maniyyatan Aikin Hajji

  • Kungiyar MURIC mai kare hakkin musulmi ta kasa ta gargadi kungiyar kwadago ta kasa ta gaggauta janye yajin aikin gama gari da ta fara a ranar Litinin
  • Daraktan kungiyar na kasa, Farfesa Ishaq Akintola ne ya yi gargadin biyo bayan yadda ya bayyana cewa yajin aikin zai kawo tsaiko babba ga jigilar alhazai
  • Shugaban ya yi takaici matuka kan yadda 'yan kungiyar suka juyar da wani jirgi da ya kamata ya dauki maniyyata aikin hajji zuwa Saudiyya ba fasinja

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja- Shahararraiyar kungiyar nan mai kare hakkin musulmi ta Najeriya (MURIC) ta bayyana takaici kan yadda yajin aikin kungiyar kwadago ta NLC zai kawo cikas ga maniyyatan aikin hajjin bana.

Kara karanta wannan

An bukaci kungiyar kwadago ta dakatar da yajin aiki saboda jigilar mahajjata

Daraktan kungiyar ta kasa, Farfesa Ishaq Akintola ya yi takaici matuka kan yadda 'yan kungiyar kwadago suka tilastawa jirgin maniyyatan aiki hajji tashi ba maniyyaci ko daya.

NLC HQ
Kungiyar MURIC ta nemi a janye yajin aiki saboda jigilar alhazai Hoto: NLC HQ/ National Hajj Commission of Nigeria
Asali: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa Farfesa Akintola ya koka kan halin da jigilar aikin hajjin bana zai fada matukar aka ci gaba da yajin aikin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

‘Lokacin yajin aiki bai kyautu ba,’ MURIC

Kungiyar kare hakkin musulmi ta bayyana lokacin da kungiyar NLC ta zaba na fara yajin aiki a kasar nan ba dace ba, kamar yadda Vanguard News ta wallafa.

Daraktan kungiyar Farfesa Ishaq Akintola ya bayyana cewa babu yadda za a yi NLC ta ce ba ta san cewa a wannan lokaci ne ake jigilar alhazan bana zuwa Saudiyya ba.

Ya ce yanzu haka iyalan maniyyatan aikin hajjin bana na cikin fargabar makomarsu matukar aka ci gaba da yajin aikin, tare da hana jirage tashi da sauka.

Kara karanta wannan

Kungiyar kwadago ta hana Alkalai zaman kotu saboda yajin aiki a Abuja

Daraktan ya gargadi kungiyar kwadago ta gaggauta janye yajin aikin ko ta fuskanci fushin musulmi a fadin kasar nan.

Farfesa Akintola na ganin son rai ne a jefa ibadar musulmi sama da 60,000 cikin garari saboda matsalar da ake fuskanta a cikin Najeriiya.

MURIC ta fadi matsayarta kan 'yan siyasa

Mun ruwaito muku yadda kungiyar kare hakkin musulmi ta Najeriya ta yi barazanar barranta kanta da duk wani dan siyasar da ba zai amfanar da musulmin kasar nan ba.

Daraktan kungiyar, Farfesa Ishaq Akintola ne ya bayyana matsayarsu, tare da Allah wadai da halin da tsohon gwamnan jihar Osun, Rauf Aregbesola ya nuna, tare da barranta musulmi da shi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel