Yajin Aikin Kungiyoyin Kwadago Ya Kawo Cikas ga Jigilar Maniyyatan Najeriya

Yajin Aikin Kungiyoyin Kwadago Ya Kawo Cikas ga Jigilar Maniyyatan Najeriya

  • Yajin aikin ƙungiyoyin NLC da TUC ya kawo tsaiko ga maniyyata sama da 60,000 zuwa ƙasa mai tsarki gudanar da aikin Hajji
  • Ma'aikatan filayen jiragen sama sun toshe hanyoyin jiragen a filayen jiragen sama na ƙasa da ƙasa a faɗin ƙasar nan tare da tilastawa jiragen komawa Saudiyya babu kowa
  • Farfesa Ishaq Oloyede, babban daraktan ƙungiyar MURIC, ya buƙaci ma’aikatan da su dakatar da yajin aikin domin ba maniyyata damar gudanar da aikin Hajji

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Yajin aikin ƙungiyoyin ƙwadago ya tilasta jiragen da suka zo ɗaukar maniyyata komawa ƙasa mai tsarki babu kowa a ciki.

Jiragen dai sun zo jigilar Alhazan Najeriya ne domin zuwa ƙasai mai tsarki gudanar da aikin Hajjin bana.

Kara karanta wannan

Yajin Aiki: Ma'aikatan gwamnati a jihar Kano sun bi umarnin kungiyoyin NLC da TUC

Yajin aiki ya hana jigilar maniyyata
Yajin aiki ya kawo cikas a jigilar maniyyatan Najeriya Hoto: @NLCHeadquarters, @HaramainInfo
Asali: Twitter

Yajin aikin da aka fara a yau Litinin 3 ga watan Yuni ya kawo cikas ga shirin na dubban Alhazan da za su je Saudiyya domin gudanar Hajjin bana.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yajin aiki ya hana jigilar maniyyata

A cewar jaridar Vanguard, ma’aikatan da ke yajin aikin a ɓangaren sufurin jiragen sama sun toshe hanyoyin jiragen sama a filayen jiragen sama na ƙasa da ƙasa a cikin ƙasar.

Ma'aikatan sun kuma hana fasinjoji shiga jiragen, tare da tilastawa matuƙan jirgin komawa Saudiyya babu kowa a ciki.

An hana aiki a filayen jirgin sama

Filayen jiragen saman da abin ya shafa sun haɗa da filin jirgin sama na Murtala Muhammed (MMIA) da ke Legas.

Bayan haka akwai filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, da filin jirgin sama na Aminu Kano, da na Yola.

Kara karanta wannan

'Yan Najeriya sun taso hadimin Tinubu a gaba kan batun yajin aikin NLC, TUC

An gano cewa sama da Alhazai 60,000 ne suka maƙale a Najeriya kuma ba za su iya zuwa ƙasar Saudiyya domin gudanar da aikin Hajjin shekarar 2024 ba.

MURIC ta buƙaci NLC ta dakatar da yajin aiki

Alhazan dai sun shafe watanni suna shirye-shiryen tafiya ƙasa mai tsarki amma a halin yanzu suna cikin halin rashin tabbas da takaici saboda yajin aikin ƙungiyar NLC.

A nasa jawabin babban daraktan ƙungiyar MURIC, Farfesa Ishaq Oloyede, ya yi kira da a dakatar da yajin aikin, inda ya ƙara da cewa yajin aikin zai shafi bikin babbar sallah mai zuwa, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.

"Muna kira ga ƙungiyoyin ƙwadago da su yi la’akari da halin da dubban Musulman Najeriya ke ciki a halin yanzu saboda yajin aikin da suke yi."
"Muna kira ga NLC/TUC da su janye yajin aikin nan take domin ba waɗannan Alhazan damar zuwa ƙasar Saudiyya domin gudanar da aikin Hajji."

Kara karanta wannan

Yajin aikin NLC da TUC ya taɓa sufurin jirgin ƙasan Kaduna zuwa Abuja

- Farfesa Ishaq Oloyede

Ƴan ƙwadago sun fatattaki jama'a

A wani labarin kuma, kun ji cewa an kwashi ƴan kallo a wani bankin Polaris da ke jihar Legas bayan da mambobin ƙungiyar ƙwadago na NLC suka dira bankin.

Ƴan ƙwadagon sun dura bankin tare da fatattakar abokan hulda domin tabbatar da bin umarnin kungiyar na shiga yajin aikin gama gari.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng