'Yan Ta'adda Sun Salwantar da Ran Basarake a Taraba Watanni 5 da Kashe Kaninsa
- 'Yan ta'adda sun jefa al'ummar kauyen Usmanu da ke jihar Taraba cikin mawuyacin hali bayan sun kai musu hari a daren Lahadi tare da kashe mai garin Auwal Abubakar
- Shugaban karamar hukumar Karim Lamido da kauyen yake, Bitrus Danjos ya tabbatarwa manema labarai harin, inda ya bayyana cewa yanzu haka jami'an tsaro na garin
- Harin da ya salwantar da rayuwar mai gari Auwal Abubakar ya zo watanni biyar bayan wasu 'yan ta'adda sun kai musu hari tare da kashe kaninsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Taraba - Al’umar kauyen Usmanu dake karamar hukumar Karim Lamido sun wayi garin Litinin cikin alhini da tsoro bayan wasu’yan bindiga sun kutsa garinsu a daren Lahadi.
Shugaban karamar hukumar, Bitrus Danjos ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun kashe mai garin Usmanu, Auwal Abubakar sannan sun tsoratar da jama’a da harbe-harbe har suka bar yankin.
Vanguard News ta wallafa cewa mutuwar mai garin ta zo masa a ba-zata cike da alhini, ganin cewar watanni biyar ke nan wasu ‘yan bindiga suka kashe kanin marigayin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Taraba na cikin dimuwar rasa Basarake,’ Danjos
Jama’ar kauyen Usmanu dake jihar Taraba sun fada cikin rudani bayan 'yan bindiga sun farmake su a daren Lahadi, inda suka kashe mai garinsu Malam Auwal Abubakar.
Shugaban karamar hukumar Karim Lamido, Bitrus Danjos ne ya shaidawa manema labarai hakan, a Litinin din nan, inda ya jaddada cewa mutanen garin na cikin firgici.
‘Yan bindiga da suka kai hari garin sun cusa tsoro a zukatan al’uma, domin da yawa daga cikinsu sun guda suna neman tsira, kamar yadda Sahara reporters ta wallafa.
Bitrus Danjos ya kara da cewa jami’an tsaro na can kauyen Usmanu din domin dawo da doka da oda, da kuma bawa mutanen garin wani nau’I na kwanciyar hankali.
An ceto dalibai a jihar Kogi
A baya mun kawo muku labarin cewa rundunar tsaron kasar nan ta samu galaba a kan miyagun da suka sace dalibai a jihar Kogi, har an ceto sauran daliban.
Kwamishinan yada labarai a jihar, Kingsley Fanwo ne ya tabbatarwa manema labarai samun nasarar, inda ya bayyana cewa wannan na nufin an ceto dalibai 30 ke nan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng