BOFIA 2020: CBN Ya Ƙwace Lasisin Wani Babban Banki a Najeriya, Ya Yi Ƙarin Bayani

BOFIA 2020: CBN Ya Ƙwace Lasisin Wani Babban Banki a Najeriya, Ya Yi Ƙarin Bayani

  • Babban bankin Najeriya CBN ya kwace lasisin bankin Heritage Plc saboda ya karya sashe na 12 (1) na dokar BOFIA 2020
  • Dokar BOFIA 2020 ta na kiyaye tsarin tafiyar da hada-hadar kudi a tsakanin bankuna da sauran cbiyoyin kuɗi na kasar
  • A wata sanarwa da bankin CBN ya fitar a yau Litinin, ya ce bankin Heritage ya gaza inganta ayyukan sa na daidaiton kudi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Babban bankin Najeriya CBN ya kwace lasisin bankin Heritage Plc, kuma bankin zai daina aiki ba tare da bata lokaci ba.

CBN ya ce ya dauki matakin domin kiyaye tsarin tafiyar da hada-hadar kudi kamar yadda aka ba da izini a ƙarƙashin sashe na 12 na dokar bankuna da sauran cbiyoyin kuɗi (BOFIA) 2020.

Kara karanta wannan

Yajin aiki: 'Yan ƙwadago sun dura ginin majalisar tarayya, sun katse wuta da ruwa

CBN ya yi magana kan hada-hadar kudin bankin Heritage
CBN ya ƙwace lasisin bankin Heritage. Hoto: @cenbank, @heritagebankplc
Asali: Twitter

A wata sanarwa da bankin CBN ya fitar a shafinsa na X a yau Litinin, ya ce an yanke hukuncin ne bayan bankin Heritage ya karya sashe na 12 (1) na dokar BOFIA 2020.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Dalilin ƙwace lasisin bankin Heritage" - CBN

Sanarwar wadda ta fito daga hannun Misis Hakama Sidi Ali, mukaddashiyar daraktan sadarwa ta babban bankin, ta ce bankin na kokarin karya tsarin hada-hadar kudi.

A cewar sanarwar:

“Hukumar gudanarwar bankin Heritage da ma kwamitin amintattu sun gaza inganta ayyukan bankin na hada-hadar kudi, wanda ya ke zama barazana ga daidaiton kudin kasar.
Duk da matakan sa ido daban-daban da CBN ya dauka domin taimaka wa bankin ya farfado, bankin Heritage ya ci gaba da aiki ba tare da wata kyakkyawar makoma ba."

Bankin Heritage ya koma karkashin ikon NDIC

Haka zalika, CBN ya ce ya dauki wannan matakin ne domin karfafa kwarin gwiwar jama’a kan tsarin banki da kuma tabbatar da cewa ba a tauye tsarin hada-hadar kudi ba.

Kara karanta wannan

Yajin aikin kungiyoyin ƙwadago ya ɗauki zafi, an rufe ofishin ministan Abuja

An nada hukumar inshorar ajiyar kudi (NDIC) a matsayin wanda bankin zai zauna a karkashinta bisa ga sashe na 12 (2) na dokar BOFIA, 2020.

Karanta sanarwar CBN a nan kasa:

'Yan sanda sun gargadi 'yan kwadago

A wani labarin, mun ruwaito cewa rundunar 'yan sandan Najeriya ta gargadi kungiyoyin kwadago kan yajin aikin da suka tsunduma a fadin kasar a yau Litinin, 3 ga watan Yunin 2024.

Rundunar ta NFF wadda ta ce yajin aikin ya sabda ka'ida da dokar kasa, ta kuma yi kira ga kungiyoyin kwadagon da su koma teburin tattaunawa da gwamnatin tarayya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel