Yajin Aikin NLC: An Rufe Tushen Wutar Lantarkin Najeriya, a Shirya Shan Duhu

Yajin Aikin NLC: An Rufe Tushen Wutar Lantarkin Najeriya, a Shirya Shan Duhu

  • Kamfanin kula da rarraba wutar lantarki na Najeriya ya sanar da jama’a cewa kungiyar kwadago ta rufe tushen wutar lantarki na kasa
  • An ruwaito cewa an rufe ginin tushen wutar da misalin karfe 2:19 na safiyar ranar Litinin, abin da ya jawo daukewar wuta a fadin kasar
  • A ranar Litinin 3 ga watan Yuni ne kungiyar kwadago ta fara yajin aikin sai baba ta gani a fadin kasar kan sabon mafi karancin albashi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

FCT, Abuja - Kamfanin kula da rarraba wutar lantarki na Najeriya ya sanar da jama’a cewa kungiyar kwadago ta rufe tushen wutar lantarki na kasa.

Kungiyar kwadago ta rufe tushen wutar a daidai lokacin da kungiyar kwadago ta NLC da TUC suka fara yajin aikin sai baba-ta-gani a fadin kasar.

TUC ta yi magana kan dauke wutar lantarki a Najeriya
Saboda yajin aikin kungiyoyin kwadago, an rufe tushen wutar lantarki na Najeriya.
Asali: Getty Images

Kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito a safiyar ranar Litinin, 3 ga watan Yuni, rufe tushen wutar ya haifar da daukewar wuta a fadin kasar.

Kara karanta wannan

Yajin aiki: 'Yan ƙwadago sun dura ginin majalisar tarayya, sun katse wuta da ruwa

An rufe ginin tushen wutar da misalin karfe 2:19 na safiyar ranar Litinin, abin da ya jawo daukewar wuta a fadin kasar kamar yadda rahoton jaridar Leadership ya nuna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yajin aiki: "An dauke wutar lantarki" - TCN

A wani bangare na sanarwar, TCN ta bayyana cewa:

“Da misalin karfe 1:15 na safiyar yau ne, jami'in kula da rarraba wuta na Benin a karkashin hukumar TCN ya sanar da cewa an kori dukkanin ma’aikata daga wajen aikin.
"An yiwa ma’aikatan da suka yi turjiya duka, inda wasu kuma suka samu raunuka a yayin da ake kokarin fitar da su daga dakin da ake kula da rarraba wutar, an bar wajen ba kowa."

An kashe tashoshin wutar lantarki

TCN ta lissafa sauran kananun tashoshin rarraba wutar da kungiyar kwadago ta rufe sun hada da Ganmo, Benin, Ayede, Olorunsogo, Akangba da Osogbo.

Kara karanta wannan

Yajin aikin kungiyoyin ƙwadago ya ɗauki zafi, an rufe ofishin ministan Abuja

Kungiyoyin kwadago sun shiga yajin aikin ne saboda gwamnati ta ki yin tayi mai gwabi kan mafi karancin albashin ma'aikata.

Majalisar tarayya ta gana da 'yan kwadago

A jiya Lahadi muka ruwaito cewa shugabannin majalisar tarayya sun gana da shugabannin kungiyar kwadago domin dakatar da ma'aikatan daga shiga yajin aiki.

Shugaban kungiyar NLC, Joe Ajaero da Festus Osifo na TUC ne suka wakilci 'yan kwadago yayin da Godswill Akpabio da Tajudeen Abbas suka wakilci bangaren majalisar tarayyar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.