Makarantu, Asibitoci, Bankuna da Sauransu Sun Tsaya Cak Saboda Yajin Aikin Ƴan Kwadago

Makarantu, Asibitoci, Bankuna da Sauransu Sun Tsaya Cak Saboda Yajin Aikin Ƴan Kwadago

  • A yau Litinin, 3 ga watan Yuni aka wayi gari da yajin aikin kungiyoyin kwadagon NLC da TUC a kusan fadin Najeriya
  • Yajin aikin ya jawo al'amura sun tsaya cak a ma'aikatun gwamnati da ke fadin kasar ciki har da makarantun da bankuna
  • Kungiyar kwadago ta shiga yajin aiki biyo bayan gaza cimma matsaya tsakanin ta da gwamnati kan karin albashi

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nigeria - A yau Litinin wa'adin da kungiyar kwadago ta ba gwamnatin Najeriya ya cika domin fara yajin aiki a fadin ƙasar.

Saboda haka kungiyar ta umurci dukkan ma'aikatun gwamnati su rufe har sai gwamnati ta saurari buƙatar su.

Kara karanta wannan

Karin albashi: Rundunar 'yan sanda ta fitar da bayanin da zai hana 'yan kwadago yajin aiki

Yajin aiki
Ma'aikatu sun tsaya cak saboda yajin aiki a Najeriya. Hoto: Emmanuel Osodi/Majority World/Universal Images Group, Krisztian Bocsi/Bloomberg
Asali: Getty Images

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa an wayi gari ma'aikatun kasar a kulle ciki har da makarantu da asibitoci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin shiga yajin aikin NLC-TUC

Tun lokacin da gwamnatin tarayya ta kara kudin wuta da janye tallafin mai kungiyar take bori a madadin ma'aikatan Najeriya.

A dalilin haka ne kungiyar ta bukaci dawo da tallafin wutar lantarki da kuma kara albashin ma'aikata ko kuma ta tsunduma yajin aiki.

Ma'aikatun da suka shiga yajin aiki

Kungiyar kwadago ta ba dukkan ma'aikatun gwamnati umurnin tsayar da aiki daga yau Litinin, 3 ga watan Yuni.

Saboda haka ma'aikatan bankuna, manyan makarantu, asibitoci, bankuna, ma'aikatan lantarki, ma'aikatan jiragen sama da na ruwa duk sun kutsa yajin aikin a yau.

Tun a ranar ma'aikata ta duniya kungiyar kwadago ta ba gwamnatin wa'adi domin kaucewa yajin aikin.

Gwamnati ta gagara shawo kan 'yan kwadago

Kara karanta wannan

Yajin aiki ya tabbata: An tashi taron NLC da majalisar tarayya ba tare da wata nasara ba

Duk da cewa gwamnatin tarayya da kungiyar sun yi zama daban daban domin samun matsaya lamarin ya gagara.

Gwamnati ya yi nufin biyan 60,000 a matsayin mafi karancin albashi amma kungiyar kwadago na harin sama da N400,000.

Atiku ya ragargaji Tinubu

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya magantu kan shekara guda da shugaba Bola Tinubu ya shafe a karaga.

Atiku Abubakar ya bayyana irin hanyoyi marasa ɓullewa da shugaba Bola Tinubu ya bi wajen kawo Najeriya halin da take ciki a yau.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng