An Jero Manyan Nasarori 7 da Tinubu Ya Samu a Kwana 365 da Ya Canji Buhari
Abuja - Gwamnatin Bola Tinubu ta shekara guda a ofis bayan karbar ragamar mulki daga hannun Muhammadu Buhari a 2023.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
A rahoton nan, Legit Hausa ta tattaro wasu daga cikin nasarorin da gwamnatin ta samu a bangarori bayan watanni 12 a ofis.
Mai taimakawa shugaban kasa wajen yada labarai, Tunde Rahman ya yi wani rubutu a Daily Trust da ya kawo wasu nasarorin.
Nasarorin gwamnatin Bola Tinubu
1. Cigaban tattalin arziki
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hukumar NBS mai tattara alkaluma ta kasa ta rahoto cewa tattalin arzikin Najeriya ya motsa da 2.98% a cikin farkon shekarar nan.
A irin wannan lokaci a shekarar bara, tattalin arzikin kasar ya motsa ne da kashi 2.31%.
2. Gangunan danyen mai
A halin yanzu, ana hako ganguna akalla miliyan 1.7 na danyen mai, hakan ya nuna an samu cigaba wajen samun kudin shiga a yau.
3. Zuba hannun jari
Hadimin shugaban kasar ya tunawa jama’a yadda aka samu ‘yan kasuwa daga kasashen waje sun zuba jarin $30bn a wannan shekarar.
4. Taso Ministoci a gaba
Shugaba Bola Tinubu ya nuna ba zai kyale duk ministan da bai yi aiki ba, tsaya masu a wuya ya zaburar da masu rike da mukamai a FEC.
5. Cigaba a birnin Abuja
Bayan nada Nyesom Wike a matsayin ministan harkokin birnin tarayya, an ga ayyuka musamman bayan cire Abuja daga asusun TSA.
6. Bangaren wutan lantarki
Duk da har yanzu ana kukan rashin wuta, an kawo doka sannan za a biya bashin da zai sa wuta ta wadaci wadanda ba su rukunin Band A.
7. Sha’anin jirgin sama
A yau an yi nasarar sasantawa da kamfanin Emirates sannan jirgin Air Peace zai fara zuwa Landan bayan gyare-gyare da aka yi a filin jirage.
Kunyar da Tinubu ya sha a mulki
Ana da labari cewa Bola Tinubu ya yi kokarin yiwa Nijar barazana saboda juyin mulki amma a karshe ya ji kunya a idon kasashen duniya.
A lokacin da Marigayi Abba Kyari yana Aso Villa, da wahala a samu bayanai ko takardun sirri sun fito, akasin abin da yake faruwa a yanzu.
Asali: Legit.ng