Dambarwar Sarauta: Kanawa Sun Nemi Taimakon Abba, Ƴan Daba Sun Mamaye Kano

Dambarwar Sarauta: Kanawa Sun Nemi Taimakon Abba, Ƴan Daba Sun Mamaye Kano

  • Mazauna garin Kano sun fara shiga fargaba kan yawaitar ƴan daba a fadin jihar musamman saboda rigimar sarauta da ake yi
  • Mutane da dama da ke Dala da Gwale da sauran yankuna sun koka kan lamarin inda suka bukaci taimakon jami'an tsaro
  • Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da dambarwar sarauta a jihar da ke kara kawo cikas a zaman lafiyarta fiye da mako ɗaya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Yayin da ake ci gaba da dambarwa kan sarautar Kano, mazauna birnin sun nuna damuwa kan tabarbarewar tsaro.

Mazauna yankin Gwale da Dala da ke Kano sun bukaci karin jami'an ƴan sanda domin inganta tsaro.

Kara karanta wannan

Yayin da ake rigimar sarautar Kano, tsaro ya tabarbare, an farmaki gidan shugaban APC

Kanawa sun nemi taimakon Abba yayin da ƴan daba suka cika Kano
Yayin da ake rigimar sarautar Kano, ƴan daba sun mamaye jihar inda aka bukaci taimakon Abba Kabir. Hoto: Sanusi Lamido Sanusi, Abba Kabir, Masarautar Kano.
Asali: UGC

Kano: Mutane sun nemi taimakon Abba

Mutane da dama sun nuna fargaba kan yadda ake samun yawaitar ƴan daba yayin da ake rigimar sarauta a jihar, cewar Daily Nigerian.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sun roki Gwamna Abba Kabir da ya kawo karshen matsalar baki daya wurin samar da ingantaccen tsaro.

Har ila yau, mazauna yankuna da dama sun bukaci a samar da isassun jami'an tsaro da za su kawo zaman lafiya a jihar duba da halin da ake ciki yanzu.

Korafin wasu masana Kano kan rashin tsaro

Wani a karamar hukumar Gwale, Abubakar Mohammed ya bayyana yadda ƴan daba suka yiwa matarsa fashi a yankin.

Har ila yau, Abdulmumin Shehu da ke Dala da Aishatu Abu da ke yankin Dan Agundi sun bukaci karin jami'an tsaro a yankin.

Wannan tabarbarewar tsaro bai rasa nasaba da rigimar da ke faruwa a jihar na sarauta wanda ya kara bullar ƴan daba.

Kara karanta wannan

Kano: Ƴan tauri sun koka a fadar Sanusi II yayin da Gwamnatin Tarayya ke gadin Aminu Ado

Yan sanda sun dakile harin yan daba

A wani labarin, kun ji cewa rundunar yan sanda ta tabbatar da dakile harin yan daba a gidan shugaban APC a Kano.

Yan daban sun yi yunkurin kutsawa gidan Abdullahi Abbas ne a ranar Juma'a 31 ga watan Mayu a karamar hukumar Gwale.

Mazauna yankin suna nuna damuwa kan yadda ƴan daba ke kara yawa musamman dalilin rigimar sarauta da ake yi a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel