Abuja: Jerin Ma’aikatu da Hukomi 25 da Kamfanin AEDC Zai Datse Wa Wutar Lantarki
- Kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja zai katse wutar wasu ma’aikatun gwamnatin tarayya da suka hada da hukumomi
- Kamfanin na AEDC ya bayyana hakan a sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, wadda ke kunshe bayanan wadanda a ke bi bashin
- Hedikwatar ‘yan sanda, barikin soji da wasu ma'aikatu 25 abin ya shafa yayin da kamfanin ya ba da wa'adin biyan basussukan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja (AEDC) ya fitar da sunayen hukumomi da ma'aikatu 25 da suka yi fice wajen kin biyan kudin wutar lantarki.
Kamfanin rarraba wutar ya ce zai katse wutar dukkanin abokan huldarsa da suka gaza biyan basussukan su nan da ranar 3 ga Yuni.
Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, abokan huldar kamfanin sun hada da barikin sojojin kasa da na sojojin sama, gwamnatin jihar Kogi, gwamnatin jihar Neja da dai sauransu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jerin ma'aikatu 25 da AEDC ke bi bashi
Duba sunayen hukumomi da ma'aikatu 25 da kamfanin zai datse wutar su idan suka gaza biyan kudin, kamar yadda jaridar The Cable ta tattara:
- Rundunar sojojin kasa ta Najeriya
- Rundunar sojojin sama ta Najeriya
- Hedikwatar tsaro (HQ)
- Hukumar raya babban birnin tarayya
- Gwamnatin jihar Kogi
- Gwamnatin jihar Neja
- Hedikwatar rundunar ‘yan sandan Najeriya
- Barikin sojojin Najeriya
- Ma'aikatar masana'antu ta tarayya
- Gidan wuta
- Ofishin sakataren gwamnatin tarayya (SGF)
- Ofishin shugaban ma'aikata
- Ma'aikatar ilimi
- Ma'aikatar harkokin mata
- Ma'aikatar masana'antu
- Ma'aikatar kasuwanci
- Ma'aikatar cikin gida
- Ma'aikatar albarkatun ruwa
- Filin wasa na kasa
- Babban dakin taron wasanni na Goodluck Jonathan
- Ma'aikatar Kudi
- Hukumar tsare-tsare ta kasa (bangaren kasafin kudi)
- Ma'aikatar ayyuka
- Hukumar kula da filayen jiragen sama ta Najeriya (FAAN) Abuja
- Dukkanin sauran abokan huldar da AEDC ke bi bashi
Anguwanni 481 aka kara wa kudin wuta
A wani labarin, mun ruwaito hukumar da ke kula da wutar lantarki ta Nijeriya, ta yi karin kudin wuta ga akalla anguwanni 481 da ke samun wutar ta awa 20 a rana.
Matakin da hukumar NERC ta dauka na kara farashin wutar lantarki ga abokan hulda na 'Band A' ya fuskanci suka daga masu ruwa da tsaki.
Asali: Legit.ng