Ana Kukan Abinci Ya Yi Tsada, ’Yan Najeriya Na Shan Lita Biliyan 1.6 Ta Madara a Shekara
- Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa 'yan Najeriya na shan lita biliyan 1.6 ta madara yayin da take kashe dala biliyan 1.5 a kowacce shekara
- Karamin ministan noma da samar da abinci, Sanata Aliyu Abdullahi ya bayyana hakan a taron bikin ranar madara ta duniya ta 2024
- Sanata Abdullahi ya ce taken bikin a Najeriya shi ne: “Samar da madara mai gina jiki da kuma nemo masu zuba jari a harkar sarrafa madara."
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Karamin ministan noma da samar da abinci, Sanata Aliyu Abdullahi, ya ce ‘yan Najeriya na shan kimanin lita biliyan 1.6 na madara a duk shekara.
Sanata Abdullahi ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a ranar Asabar a Abuja domin bikin ranar madara ta duniya ta 2024.
![](https://netstorage-legit.akamaized.net/images/54450451cce91bd2.jpg?impolicy=cropped-image&imwidth=256)
Kara karanta wannan
Aikin Hajji: Najeriya na shirin kafa asibitoci a Makkah, ta na jiran amincewar Saudiyya
![Gwamnati ta yi magana kan samar da madara a Najeriya Gwamnati ta yi magana kan samar da madara a Najeriya](https://netstorage-legit.akamaized.net/images/db59ccec2704784b.jpg?imwidth=900)
Asali: Getty Images
Karamin ministan ya ce kashi 60 na kayayyakin madara ana shigo da su ne daga kasashen waje, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
2024: Bikin ranar madara ta duniya
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN), ya ruwaito cewa, 1 ga watan Yuni, ita ce ranar da aka kebe domin bikin ranar madara ta duniya.
Taken bikin ranar madara ta duniya a bana shi ne: "Mu yi bikin murnar sarrafa madara mai gina jiki da dorewa."
Sanata Abdullahi ya ce taken bikin a Najeriya shi ne: “Samar da madara mai gina jiki da kuma nemo masu zuba jari a harkar sarrafa madara."
2024: An sha lita 1.6b ta madara a Najeriya
Jaridar PM News ta ruwaito ministan na cewa Najeriya na kashe dala biliyan 1.5 a duk shekara wajen shigo da kaso 60 na madara da kayayyakin ta.
![](https://netstorage-legit.akamaized.net/images/d490e83403d798dd.jpg?impolicy=cropped-image&imwidth=256)
Kara karanta wannan
Gwamantin tarayya da fadi matakan da ta dauka domin rage hauhawar farashin abinci
“Wannan ya faru ne saboda gibin da ake samu wajen samar da madara a kasar, yayin da ‘yan Najeriya ke shanye akalla lita biliyan 1.6 na madara da kayayyakin ta a shekara.
"Burin shugaban kasa Bola Tinubu shi ne mu samu wadataccen abinci a kasa ta yadda za mu rika fitar da kayayyakin madara zuwa kasashen Afirka a karkashin yarjejeniyar AfCFTA)."
- In ji Sanata Abdullahi.
Sarrafa rogo zuwa sinadarin fetur a Enugu
A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnatin tarayya da ta jihar Enugu sun kulla yarjejeniyar noman rogo da sarrafa shi zuwa sinadarin fetur.
Wannan yarjejeniyar wadda aka yi nasara a matakin gwaji, za ta taimaka wajen habaka noman rogo da bunkasa tattalin arziki, tare da magance rashin aikin yi da rashin tsaro.
Asali: Legit.ng