Wata sabuwa: Gwamnatin tarayya za ta haramta shigo da madara da kifi, ta fadi dalili

Wata sabuwa: Gwamnatin tarayya za ta haramta shigo da madara da kifi, ta fadi dalili

- Gwamnatin tarayya ta ce tana shirin haramta shigo da kifi da madara

- Ministan noma, Nanono ne ya bayyana hakan a garin Dutse, babbar birnin jihar Jigawa

- Ya ce za a samar da cibiyoyin sarrafa madara a kasar domin akwai kimanin shanaye miliyan 25 a cikinta

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa kwanan nan za ta hana shigo da kifi da madara cikin kasar.

Ministan noma, Sambo Nanono ne ya bayyana hakan a wani taron kaddamar da cibiyar raya kasuwancin noma a jami’ar tarayya ta Dutse, jihar Jigawa.

Ya ce gwamnatin tarayya za ta yi nazari sosai a kan duk wasu hanyoyi na shigo da abinci cikin kasar, Radio Nigeria ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Zaben Edo: PDP ta jinjinawa Buhari kan wani ƙoƙari da ya yi

Wata sabuwa: Gwamnatin tarayya za ta haramta shigo da madara da kifi, ta fadi dalili
Wata sabuwa: Gwamnatin tarayya za ta haramta shigo da madara da kifi, ta fadi dalili Hoto: Daily Trust
Source: Getty Images

Ya ce Najeriya na da kimanin shanaye miliyan 25 a kasar kuma lita biyar kawai ake amfani dashi na madara a kullun.

Nanono ya ce matsala guda da kasar ke fuskanta shine na sarrafa madara.

Ya ce gwamnatin tarayya ta fara wani shiri na bude cibiyoyin sarrafa madara domin hana shigo da madara cikin kasar.

A cewarsa, akwai wadannan cibiyoyi fiye da guda bakwai kuma za a bunkasa wasu a kasar.

Nanono ya ce cibiyar na Dawakin-Kudu a Kano kadai yana da Fulani makiyaya fiye da dubu goma sha biyu a yankin.

A wani labari makamancin haka, Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata, ya ce gwamnatin tarayya ta hana shigo da kayan abinci ne domin ta bunkasa aikin noma tare da tseratar da 'yan Najeriya daga rashin aikin yi.

Ya jaddada cewa, noma babbar hanya ce ta samar da ababen bukata, rage zaman kashe wando da fatattakar talauci daga kasar nan, Channels TV ta wallafa.

"Domin ganin mun dawo da samar da kayan bukata, dole ne marasa aikin yi ballantana wadanda basu yi karatu ba su fada harkar noma.

"Da ace bamu koma gona ba, da yanzu muna cikin matsala. Hakan ne yasa dole aka haramta shigo da kayayyakin abinci domin samar da aiki," shugaban kasa yace.

KU KRANTA KUMA: Kada ku karya tattalin arzikin Najeriya da korona - Majalisar dattawa

Shugaban kasar ya bayyana hakan ne yayin wani taro da yayi ta yanar gizo da kwamitin bada shawara a kan tattalin arziki a gidan gwamnati da ke Abuja.

Shugaban kasar ya kara da bayyana dalilinsa na karbo bashi domin samar da ababen more rayuwa. Ya ce gwamnatinsa tana cin bashin ne domin 'yan kasar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel