Yajin Aikin Ƴan Ƙwadago: Hukuma ta Bayyana Makomar Masu Jarrabawar WAEC

Yajin Aikin Ƴan Ƙwadago: Hukuma ta Bayyana Makomar Masu Jarrabawar WAEC

  • Hukumar shirya jarrabawar kammala sakandare ta WAEC ta bayyana matsayarta kan fara rubuta jarrabawa da daliban kasar nan za su yi yayin da za a fara yajin aiki
  • A ranar Litinin da za a shiga yajin aikin sai baba ta gani ne dalibai a yankin Afrika ta yamma za su fara rubuta jarrabawar WAEC a fadin nahiyar
  • Jami'ar hukumar da ke kula da jihar Ekiti T.A.Y Lawson ta bayyana cewa yajin aikin ba zai shafi rubuta jarrabawar ba saboda ba a Najeriya ne kawai ake yin ta ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Ekiti- A lokacin da dalibai suka fara fargabar makomar jarrabawarsu ta kammala sakandare WAEC saboda yajin aikin kungiyoyin kwadago, hukumar shirya jarrabawar ta magantu.

Kara karanta wannan

"Shugaba Tinubu ya saba doka", Kungiyar lauyoyi za ta kotu saboda an sauya taken Najeriya

Jami'a mai kula da hukumar reshen jihar Ekiti, T.A.Y Lawson yajin aikin gama-garin da za a fara ranar Litinin ba zai hana dalibai fitowa domin rubuta jarrabawar ba.

Jarrabawar WAEC
Hukumar shirya WAEC ta sanar da dalibai su fito jarrabawa ranar Litinin Hoto: Waec
Asali: Facebook

The Nation ta tattaro cewa hukumar ta bayyana cewa tana da masaniya kan shirin tsunduma yajin aikin sai baba-ta-gani da kungiyoyin kwadago za su fara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin rubuta WAEC duk da yajin aiki

Hukumar shirya jarrabawar kammala makarantar sakandare ta WAEC ta bayyana dalilinta na cewa dalibai su fito su rubuta jarrabawarsu ranar Litinin duk da yajin aiki.

Jami'ar hukumar da ke kula da jihar Ekit, T.A.Y Lawson ta bayyana cewa duk da sun tare da kungiyar kwadago 100%, amma bai kamata daliban su rasa jarrabawarsu ba, kamar yadda The Guardian ta wallafa.

Ta ce tunda ana rubuta jarrabawar WAEC a dukkanin kasashen dake Afrika ta yamma, bai kamata daliban Najeriya su rasa rubuta ta su ba.

Kara karanta wannan

"Karancin kudi": Kungiyar ASUU ta tsunduma yajin aiki a jami'ar Kano, ta bayyana dalili

Saboda haka ne T.A.Y Lawson ta umarci iyaye, malamai, masu duba jarrabawa da dalibai su kwana cikin shirin rubuta jarrabawar kamar yadda aka tsara tun da fari.

WAEC ta rike sakamakon jarrabawa

A baya mun kawo muku rahoton cewa hukumar shirya jarrabawar WAEC a kasar Ghana ta rike sakamakon jarrabawar wasu dalibai daga makarantu 235 a kasar.

Jami'in hulda da jama'a na hukumar a Ghana, John Kapi ya ce an hana su sakamakon jarrabawar ne saboda ana zarginsu da amfani da fasahar AI wajen amsawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.