Yadda Shugaba Tinubu ya Jefa Kan Shi a Matsala Wajen Nadin Mukamai a Makarantu

Yadda Shugaba Tinubu ya Jefa Kan Shi a Matsala Wajen Nadin Mukamai a Makarantu

  • Bayan tsawon watanni, Bola Ahmed Tinubu ya nada shugabannin da za su kula da jami’o’in gwamnatin tarayya a kasar
  • Nadin mukaman da aka yi ya shafi manyan makarantun gaba da sakandare wadanda ake koyon ayyuka (Polytechnic)
  • Wasu suna ganin Bola Tinubu bai nemi zaman lafiya wajen yadda ya yi nadin ba, hakan ya jawo masa surutun jama’a

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Nadin da Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya yi a manyan makarantun gaba da sakandare ya jawo surutu a Najeriya.

Shugaban kasar ya nada shugabannin da za su kula da majalisun da ke sa ido wajen gudanar da jami’o’i da manyan makarantu.

Bola Tinubu
Mukaman da Bola Tinubu ya ba da a makarantun Najeriya ya jawo magana Hoto: @AjuriNgelale
Asali: Twitter

Jami'o'i da makarantu sun soki gwamnatin Tinubu

Nade-naden mukaman da aka sanar a X ya shafi jami’o’in gwamnati da makarantun koyon aiki da aka fi sani da Polytechnic 111.

Kara karanta wannan

Abubuwan kunya 6 da suka faru da Gwamnatin Tinubu a cikin shekara 1

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Legit Hausa ta fahimci cewa hankalin mutane da yawa bai kwanta ba musamman la’akari da wadanda gwamnati ta ba mukaman.

Kafin nan dama an dade ana jiran shugaba Bola Tinubu ya yi wadannan nadin domin a ji dadin gudanar da harkokin makarantun.

Nade-naden da Tinubu ya yi a jami'o'i

Alal misali, tsohon ministan kasafi, Sanata Udo Udoma zai jagoranci majalisar da za ta kula da jami’ar Bayero da ke garin Kano.

A nadin jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, kusan Mahmud Yayale Ahmad ne kadai fitaccen mutumin Arewa da aka dauko.

Sauran wadanda za su rika sa ido a harkar fitacciyar jami’ar su ne: Rufus Bature, Aisha Oni da kuma Rt. Hon. Mathew Akpan.

Da aka tafi jami’ar aikin gona ta Ogun, sai aka dauko Yusuf Ali, Farfesa Muhammad Auwal Husseini, Zubairu Aliyu da Abubakar Jalo.

Kara karanta wannan

‘Yan Najeriya sun zabi Ministocin da za a kora da wadanda Tinubu zai bari a ofis

Za a samu irin wannan koke-koke a jami’ar tarayya da ke garin Dutse a jihar Jigawa.

Shugaba Tinubu ya ba Jakada mukami

Shugaban APC na jihar Kaduna, Air Comodore Emmanuel Jakada ya samu babban matsayi a jami’ar fasaha ta ATBU a Bauchi.

Sauran ‘yan majalisarsa a jihar Bauchi su ne: Engr. Usua Charles Akpan, Lanre Tojeshu, Modu Mustapha da Olusegun White.

Tinubu ya ba Shinkafi, Yuguda mukami

An ji labari tsohon gwamnan Zamfara, Mahmud Shinkafi zai jagoranci jami’ar Jos.

Shi kuma tsohon gwamnan Bauchi watau Malam Isa Yuguda ya samu mukami a jami’ar tafi da gidanka da aka fi sani da NOUN.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng