Kano: Hakimai da Shugabannin Kananan Hukumomi 44 Sun Ziyarci Sanusi II, Fada Ta Cika Maƙil

Kano: Hakimai da Shugabannin Kananan Hukumomi 44 Sun Ziyarci Sanusi II, Fada Ta Cika Maƙil

  • Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II ya karbi hakimai da shugabannin ƙananan hukumomi 44 da ke jihar Kano
  • Hakiman da shugabannin riko na kananan hukumomin sun kawo caffan ban girma ne ga Sarkin a yau Juma'a 31 ga watan Mayu
  • Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba dambarwa kan sahihin sarki a jihar Kano bayan tube sarkin na 15, Aminu Ado Bayero

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Hakimai da shugabanni riko na kananan hukumomi 44 a jihar Kano sun kai ziyara ga Muhammadu Sanusi II.

Hakiman da shugabannin kananan hukumomin sun kai caffan ban girma ga Sarkin Kano na 16 domin nuna masa goyon baya.

Kara karanta wannan

Bidiyon dubban mutane da suka tari Sarkin Kano bayan Juma'a, ya aika sako a huduba

Hakimai sun kai caffan ban girma ga Sanusi II a Kano
Hakimai da shugabannin kananan hukumomi 44 sun kai wa Sanusi II ziyara a fadarsa. Hoto: @Opeyemtech.
Asali: Twitter

Kano: Ziyarar Hakimai wajen Sanusi II

Daily Nigerian ta tattaro cewa hakiman sun kai ziyarar a yau Juma'a 31 ga watan Mayu a fadarsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wata majiya ta tabbatar da cewa duka hakiman sun taho da dagatansu a ƙauyuka domin yin mubaya'a ga sabon Sarkin.

Har ila yau, an tabbatar su ma shugabannin ƙananan hukumomin sun zo da duka kansilolinsu zuwa fadar.

Hakimai sun yi mubaya'a ga Sanusi II

"Daukacin hakimai da shugabannin riko na kananan hukumomi 44 sun kawo caffan ban girma ga Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II."
"Hakiman sun zo da dagatai daga kauyukansu yayin da shugabannin suka zo da kansilolinsu da sauran mambobi."
"Yau fadar ta cika makil, inda suka tabbatar da Muhammadu Sanusi II a matsayin sarkin Kano."

- Majiyar

Aminu Ado ya cigaba da zaman fada

Duk da haka, sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero yana ci gaba da karbar baki a fadarsa da ke Nasarawa tun bayan dawowa jihar bayan tube shi a sarauta.

Kara karanta wannan

"Dalilin da ya sa har yanzu Aminu Ado Bayero yake halastaccen Sarkin Kano"

Yanzu haka dai maganar masarautun Kano da aka ruguza tana gaban kotu.

Sarkin Kano ya jagoranci sallar Juma'a

A wani labarin, kun ji cewa Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya jagoranci sallar Juma'a a babban masallacin Kano.

Yayin da yake dawowa daga masallacin, dubban mutane ne suka tarbe shi domin nuna goyon baya gare shi.

Sanusi II yayin gudanar da huduba a masallacin Juma'a ya yi magana kan imani da ƙaddara ba tare da ja da hukuncin Allah kan haka ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.