"Shugaba Tinubu ya Saba Doka", Kungiyar Lauyoyi Za Ta Kotu Saboda Sauya Taken Najeriya

"Shugaba Tinubu ya Saba Doka", Kungiyar Lauyoyi Za Ta Kotu Saboda Sauya Taken Najeriya

  • Masu rajin inganta harkokin shari'a a majalisa ta bayyana hanyar da aka bi wajen sauya taken Najeriya da cewa ya sabawa dokar kasa
  • Kungiyar ta kuma bayyana shirinta na maka shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da daukacin wadanda suka taimaka masa gaban kotu
  • Sakataren kungiyar, Tonye Jaja ya shaidawa manema labarai cewa dole ne sai shugaban kasar da 'yan majalisa sun nemi ra'ayin 'yan Najeriya kafin sauyin

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja- Wata kungiya mai rajin inganta harkokin shari'a a majalisa ta Association of Legislative Drafting and Advocacy Practitioners, ta bayyana cewa matakin da 'yan majalisa da shugaba Bola Tinubu suka dauka na sauya taken Najeriya ya saba doka.

Kara karanta wannan

Taken Najeriya: Tinubu ya yi karin haske kan hikimar komawa tsohon taken kasa

Kungiyar ta kuma ce ta kammala dukkanin shirye-shiryen maka shugaban kasa da duk wadanda ke da hannu cikin sauya taken a gaban babban kotun tarayya.

Bola Ahmed Tinubu
Lauyoyi za su maka shugaban Najeriya, Bola Tinubu gaban kotu kan sauya taken kasar ba bisa ka'ida ba Hoto: NGRPresident
Asali: Facebook

The Cable ta wallafa cewa a sanarwar da sakataren kungiyar, Tonye Jaja ya sanyawa hannu a ranar Juma'a, ba a bi hanyoyin da suka dace ba wajen dawo da tsohon taken ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Taken Najeriya: Wadanne ka'idoji Tinubu ya saba?

Kungiyar da mafi akasarin 'ya 'yanta lauyoyi ne ta bayyana wasu ka'idoji da ta ce 'yan majalisa da shugaban kasa sun tsallake.

Punch News ta wallafa cewa majalisa ba ta ji ra'ayoyin al'umar kasa ba kamar yadda sashe na 60 na kundin tsarin mulkin Najeriya ya zayyana.

Sanarwar da sakataren kungiyar, Tonye Jaja ya fitar, ta ce sai da aka kira jama'ar kasar nan kafin samar da sabon yake a shekarar 1978.

Kara karanta wannan

Diyar Ado Bayero ta turawa Tinubu da Abba sako, tayi zancen rigimar masarautar Kano

Haka kuma kungiyar ta gano cewa shugaban kasa bai mika takarda kan neman canjin zuwa majalisa da shugaban majalisar wakilai ba.

Kungiyar ta koka kan makudan kudin da ta ce za a kashe wajen tabbatar da sabon taken ya zagaye ofisoshin gwamnatin.

Tsohuwar minista ta fusata kan taken Najeriya

A baya mun baku labarin cewa tsohuwar ministan ilimin Najeriya Obiageli Ezekwesili ta barranta kanta da sabon taken Najeriya da Bola Tinubu ya dawo da shi.

Ministar ta bayyana takaicin yadda aka dawo da tsohon taken da turawa suka hadawa kasar, tare da cewa ba za ta taba rera taken 'Nigeria we hail thee' ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel