'Yan Kwadago Sun Ayyana Shiga Yajin Aikin Sai Baba Ta Gani Kan Abubuwa 2 a Najeriya

'Yan Kwadago Sun Ayyana Shiga Yajin Aikin Sai Baba Ta Gani Kan Abubuwa 2 a Najeriya

  • Ƴan kwadago a Najeriya sun sanar da shiga yajin aiki daga ranar Litinin, 3 ga watan Yuni, 2023 saboda gazawar gwamnatin tarayya
  • NLC da TUC sun ɗauki wannan matakin kan rashin karkare batun mafi ƙarancin albashi da kuma ƙarin kuɗin wutar lantarki ga ƴan Band A
  • Gwamnati ta gabatar da tayin N60,000 a matsayin ƙarancin albashi amma NLC ta tsaya kai da fata kan N494,000

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Kungiyoyin kwadagon Najeriya sun ayyana shiga yajin aikin sai baba-ta-gani a fadin kasar nan daga ranar Litinin 3 ga watan Yuni, 2024.

Ƴan kwadagon sun ɗauki matakin tsunduma yajin aiki ne kan gazawar gwamnatin tarayya na ƙarƙare batun mafi karancin albashi da ƙara kuɗin lantarki.

Kara karanta wannan

Kotu ta kori ƴan APC 25, ta hana su ayyana kansu a matsayin 'yan majalisa

NLC da TUC sun shiga yajin aiki.
Ma'aikatan Najeriya sun ayyana shiga yajin aikin sai baba-ta-gani daga ranar Litinin Hoto: Nigeria Labour Congress
Asali: Twitter

Jaridar Vanguard ta tattaro cewa tun da farko manyan kungiyoyin kwadagon ƙasar nan NLC da TUC sun nun alamun fara yajin aiki daga farkon makon gobe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƙungiyoyin sun nuna cewa matuƙar kwamitin mafi ƙarancin albashin da gwamnati ta kafa ya gaza amincewa da buƙatun ƴan kwadago, to tabbas za su shiga yaji.

NLC da TUC sun shiga yajin aiki

Shugabannin NLC da TUC, Joe Ajaero da Festus Osifo, sun tabbatar da za a tafi yajin aiki a wani taron manema labarai da suka gudanar a Abuja yau Jumu'a.

Manyan jagororin ƴan kwadagon biyu sun ce za a fara yajin aikin ne da tsakar daren ranar 2 ga watan Yuni, cewar The Nation.

Sun buƙaci rassan su na jihohi, ƙungiyoyin fararen hula da ƙawayensu, ƴan kasuwa maza da mata da su shirya tsaida kmai cak a ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Tinubu ya samu sauƙi a bukatar da ƴan ƙwadago suka gabatar kan mafi ƙarancin albashi

Shugaban TUC, Osifo ya ce gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu sun kafe kan N60,000 da suka gabatar a taron ranar Talata. 

"Za mu fara yajin aiki na daga ranar Lahadi da tsakar dare, 2 ga Yuni, 2024 kuma ba zamu ɗaga ƙafa ba har sai mun samu sabon mafi karancin albashi," in ji shi.

ASUU ta shiga yajin aiki a Kano

A wani rahoton kuma kungiyar malaman jami'o'i (ASUU) reshen jami'ar Yusuf Maitama Sule da ke jihar Kano ta shiga yajin aikin gargadi na mako biyu.

A cikin wata sanarwa daga shugabannin kungiyar, sun shiga yajin aikin ne saboda karancin kudin da suke samu daga gwamnati.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel