Sarautar Kano: Hakimai Sun Rude Kan Sarkin da Za Su Bi, Wasu Sun Shiga Rububi
- Wasu hakimai da masu rike da masarautun gargajiya a jihar Kano sun rasa layin da za su kama kan rigimar da ake yi
- Duk da wasu daga cikinsu sun yi mubaya'a ga Muhammadu Sanusi II amma akwai wadanda ke tare da Aminu Ado Bayero
- Sai dai kuma akwai wadanda suka rasa layin da za su bi inda suka janye jikinsu a rigimar domin ganin karshen lamarin
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Yayin da ake ci gaba da dambarwar sarautar Kano, wasu hakimai da masu saurautar gargajiya sun shiga rudani.
Wasu da dama daga cikin hakimai da masu rike da masarautun gargajiya sun rasa wanda za su yiwa mubaya'a.
Kano: Hakimai sun shiga rudani kan sarauta
Duk da wasu da dama da suka rasa kujerunsu bayan dokar Majalisa, sun yi mubaya'a ga Muhammadu Sanusi II, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai akwai wadanda suka rasa madafa inda suke jira sai komai ya daidaita an samu maslaha kafin su nuna bangaren da suke.
Har ila yau, akwai wasu masu rike da masarautun gargajiya da ke mubaya'a ga dukan bangarorin wurin tura wakilai a ko ina domin gudun kada ta kwaye.
Gwamnatin Kano ta ba sarakai umarni
Wannan na zuwa ne bayan gwamnatin jihar ta umarci duka masu masarautun gargajiya su koma bayan Muhammadu Sanusi II.
Sai dai duk da umarnin gwamnatin jihar, Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero na ci gaba da karbar wasu hakimai a fadar Nasarawa.
Misali tsohon hakimin Bichi kuma Barden Kano, Idris Bayero har yanzu ba a ji ɗuriyarsa ba kan rigimar da ake yi.
Dubban jama'a sun tarbi Sarki Sanusi II
Kun ji cewa dubban mutane ne suka tarbi Muhammadu Sanusi II bayan kammala sallar Juma'a a yau a birnin Kano.
Mutanen sun fito kwansu da kwarkwata yayin da suke nuna tsantsar goyon bayan ga sabon Sarkin a jihar.
Wannan na zuwa ne yayin da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero shi ma ya yi tasa sallar Juma'a a wani masallaci daban.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng