"Ba Wanda Zai Ja da Hukuncin Allah," Sanusi II Ya Yi Magana Mai Ratsa Zuciya a Huɗubar Jumu'a

"Ba Wanda Zai Ja da Hukuncin Allah," Sanusi II Ya Yi Magana Mai Ratsa Zuciya a Huɗubar Jumu'a

  • Sarki Muhammadu Sanusi II ya jagoranci sallar Jumu'a a babban masallacin Ƙofar Kudu a Kano kuma ya yi huɗuba kan imani da Allah
  • Basaraken ya bayyana cewa babu wanda zai ja da hukuncin Allah, inda ya ƙara da cewa komai ka ga ɗan adam ya samu ko ya rasa daga Allah ne
  • Sanusi II ya kuma ja hankalin musulmai cewa watan Zhul Hajj ya kusa shiga don haka ya kamata kowa ya dage da ibada a kwanakin farko

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano - Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II ya ce babu wanda ya isa ya tuhumi Allah kan kowane irin lamari da ya aiwatar.

Basaraken ya faɗi haka ne a hudubar Sallar Jumu'a da ya gabatar a babban masallacin Jumu'a na Ƙofar Kudu a jihar Kano a yau.

Kara karanta wannan

Taken Najeriya: Tinubu ya yi karin haske kan hikimar komawa tsohon taken kasa

Muhammadu Sanusi II.
Muhammadu Sanusi II ya jagoranci sallar Jumu'a a masallacin fadar Kofar Kudu Hoto: Masarautar Kano
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa hudubar Sarkin ta yau ta maida hankali ne kan imani da Allah a kowane yanayi mutum ya tsinci kansa, na farin ciki ko jarabawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hudubar Juma'ar Muhammadu Sanusi

"Duk wanda ya yi imani Allah ne kaɗai mai bayar wa, to dole zai rungumi duk wani hukuncin Allah da hannu bibbiyu. Babu wanda zai tuhume Allah dalilim faruwar wani abu.
"Mun sani cewa duk wanda bai yarda da kaddara ba to imaninsa bai cika ba, ya kamata mu godewa Allah a kowane hali muka shiga.
"Dole mu yi imani cewa duk abin da muka samu daga Allah ne kuma duk abin da muka rasa daga gare shi ne. Watan Zhul Hajj ya kusa kuma yana da falala, dole mu dage da ibada a wannan kwanakin."

- Muhammadu Sanusi II.

Kara karanta wannan

"Dalilin da ya sa har yanzu Aminu Ado Bayero yake halastaccen Sarkin Kano"

Bayan haka ne mai martaba sarkin ya jagoranci Sallah raka'a biyu ta Jumu'a a masallacin fadar Ƙofar Kudu.

'Yan sanda sun raba gardamar sarautar Kano

A ɗazu rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta musanta rahotannin da ke cewa Ado Bayero zai jagoranci Sallar Juma’a a babban masallacin Kofar Kudu da ke Kano.

Sanusi II da Aminu Ado Bayero su na da'awar su ne rike da iko, lamarin da ya haifar da rudani a cikin birnin Kano.

Rikicin sarautar dai na ci gaba da ƙamari tun bayan dawo da Sarki Sanusi II da kuma rusa masarautun nan biyar.

Wanene sahihin Sarkin Kano?

A wani rahoton kuma wani lauya a jihar Kano, Umar Sa'ad Hassan, ya yi bayanin cewa har yanzun Alhaji Aminu Ado Bayero ne halastaccen Sarki.

Umar Hassan ya bayyana cewa babbar kotun tarayya mai zama a jihar ta ba da umarnin dakatar da mayar da Muhammadu Sanusi kan sarauta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel