EFCC ta Fara Binciken Sanata Rabi'u Kwankwaso kan Zambar Kudin 'Yan Fansho

EFCC ta Fara Binciken Sanata Rabi'u Kwankwaso kan Zambar Kudin 'Yan Fansho

  • Rahotanni na bayyana cewa hukumar hana yiwa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa (EFCC) ta gayyaci tsohon gwamnan Kano kan zamba
  • An gayyaci Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso domin bayar da bayanai kan zargin da ake yi masa na almundahanar kudin 'yan fansho
  • Amma babban mai ba gwamnan Kano shawara kan kafafen yada labarai Bashir Sanata ya shaidawa Legit cewa duk bita da kullin siyasa ce kawai

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja-Hukumar hana yiwa tattalin arzikin na kasa ta’annati (EFCC) ta mika goron gayyata ga jagoran APC, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.

Hukumar ta bude binciken tsohon gwamnan na Kano da zambar kudin fansho da yawan su ya kai N2.5bn.

Kara karanta wannan

ISWAP ta ba mazauna garin Kukawa zabin barin gidajensu ko a kashe su

Rabiu Musa Kwankwaso
EFCC gayyaci Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso kan badakalar kudin 'yan fansho Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Asali: Facebook

Punch ta wallafa cewa tuni hukumar EFCC ta gayyaci Rabi’u Musa Kwankwaso, tare da yi masa tambayoyi kan zargin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwankwaso ya ba EFCC bayanai

Wata majiya a hukumar ta EFCC ta bayyana cewa Sanata Kwankwaso ya yi tattaunawar keke-da-keke da masu bincike a hukumar.

Majiyar ta kuma kara da cewa tsohon gwamna a Kano, Kwankwaso ya bayar da muhimman bayanai kan zargin da ake yi masa na sama da fadi da kudaden ‘yan fansho.

Wata majiyar ta bayyana cewa za su ci gaba da binciken Rabi’u Musa Kwankwaso kan batun, kamar yadda Vanguard News ta wallafa.

‘Bita da kulli ake yiwa Kwankwaso,’ - Hadimi

Babban mashawarcin gwamna Abba Kabir Yusuf kan kafafen yada labarai, Bashir Sanata ya yi zargin ana binciken ne domin rage kimar Kwankwaso.

Amma ya ce ko kadan hakan ba zai rage kimarsa a idanun wadanda suka san shi ba, ganin cewar ba shi da son zuciyar da zai kwashi dukiyar talakawa.

Kara karanta wannan

An bayyana abin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya Tattauna da Nuhu Ribadu

Sanata ya ce ciki da gaskiya, wuka ba ta huda shi, ya kuma ce har gobe suna tare da jagoransu, wanda a cewarsa magauta ne suke ta neman kai shi kasa.

EFCC za ta fara binciken Kwankwaso

A baya mun kawo muku labarin cewa hukumar hana yiwa tattalin arzikin kasa ta'annati ta EFCC ta dauko binciken tsohon gwamnan Kano Rabi'u Musa Kwankwaso.

An fara binciken ne a lokacin da ake tsaka da dambarwar masarautar Kano da ake ganin jagoran NNPP na da hannu a ciki, lamarin da ya musanta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.