Masarautar Kano: Aminu Bayero Zai Jagoranci Sallar Juma’a? ’Yan Sanda Sun Magantu

Masarautar Kano: Aminu Bayero Zai Jagoranci Sallar Juma’a? ’Yan Sanda Sun Magantu

  • Jita-jitar da ake yadawa cewa sarkin Kano na 14, Aminu Bayero ne zai jagoranci sallar Juma'a a babban masallacin fada ba gaskiya ba ne
  • Rundunar 'yan san Kano ta nemi jama'a da suyi watsi da wannan jita-jitar tana mai cewa Aminu Bayero zai yi Juma'a ne a fadar Nasarawa
  • A hannu daya kuma kwamishinan ‘yan sandan jihar, Usaini Gumel, ya shaida Sarki Sanusi II zai yi sallar Juma'a a masallacin da ke fada

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Kano - Jita-jita ta karade kafofin sada zumunta cewa sarkin Kano na 14, Aminu Ado Bayero ne zai jagoranci sallar Juma'a a babban masallacin fada.

Wannan na zuwa yayin da wasu masu goyon bayan Aminu Bayero suka shirya yin gangamin raka basaraken zuwa masallacin fada a yau Juma'a.

Kara karanta wannan

Kano: Tashin hankali yayin da Sarki Sanusi II da Aminu Ado ke shirin sallar Jumu'a

'Yan sanda sun yi magana kan limanci a masallacin Kano
'Yan sanda sun karyata jita-jitar Aminu Bayero zai yi limanci a masallacin Kano.
Asali: Twitter

Wani Aminu Dahiru Ahmad, ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa za su yi gangamin rakiyar ne da misalin karfe 12:30 na ranar Juma'ar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Aminu Dahiru Ahmad yana tare da APC kuma yana cikin masoyan Aminu Bayero.

"Kowa ya zo rakiyar mai martaba Sarkin Kano Aminu Ado Bayero."

- Aminu Dahiru Ahmad

Aminu Bayero zai jagoranci sallar Juma'a?

Sai dai ana haka ne kuma rundunar 'yan sandan jihar Kano ta karyata wannan jita-jita ta cewa Aminu Ado Bayero ne zai jagoranci sallar Juma'a a babban masallacin Sarki.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Usaini Gumel, ya karyata hakan a hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ta wayar tarho a ranar Juma’a.

Usaini Gumel ya bayyana cewa Bayero zai yi sallar Juma’a ne a masallacin da ke cikin fadar Nasarawa, inda yake zaune a halin yanzu, in ji rahoton jaridar Trinubune.

Kara karanta wannan

Duk da umarnin kotu da ke neman sauke Sanusi II, Mataimakin Gwamna ya gana da Sarki

Sanusi II zai jagoranci sallar Juma’a

Kwamishinan ya ce ‘yan sanda da sauran jami’an tsaron jihar za su samar da ingantaccen tsaro a fadar Sarkin Kano, inda ake sa ran Sarki Muhammad Sanusi II zai yi sallar Juma’a.

“Rundunar ‘yan sanda ta bukaci jama’a da su yi watsi da wannan rahotan karyar da ke yawo a intanet, kuma jama'a su ci gaba da harkokin gaban su ba tare da wata fargaba ba.
“’Yan sanda za su tabbatar da jama'a sun gudanar da sallar Juma’a cikin kwanciyar hankali ba tare da barazana ga rayuka da dukiyoyinsu ba.”

- Kwamishinan 'yan sandan Kano

Matsayin babbar kotun tarayya da ta jiha

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Barista Wale Adeagbo ya ce dokar kasa ba ta fifita babbar kotun tarayya a kan babbar kotun jiha ba.

Barrister Wale Adeagbo ya na tsokaci ne kan umarnin da kotunan biyu suka bayar kan rigimar masarautar Kano tsakanin Sarki Muhammadu Sanusi II da kuma Aminu Ado Bayero.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel