Tinubu Ya Dauki Zafi Kan Ministocinsa, Ya Fadi Wadanda Zai Kora Daga Mukamansu
- Shugaban kasa, Bola Tinubu ya tabbatar da aniyarsa ta korar ministocin da suka gaza yin katabus a gwamnatinsa
- Tinubu ya godewa duka ministocinsa saboda kokarin da suke yi sai dai ya ce zai sallami duk wanda ya gaza yin wani abin kirki ga ƴan Najeriya
- Shugaban ya bayyana haka ne a yau Alhamis 30 ga watan Mayu yayin taro da shugabannin Arewa Consultative Forum
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya tabbatar da cewa zai kori duka ministocinsa da ba su tabuka komai ba.
Shugaban kasar ya bayyana cewa zai ci gaba da kawo ababan more rayuwa ga al'ummar Najeriya baki daya.
Tinubu ya godewa ministocinsa kan kokarinsu
Tinubu ya fadi haka ne yayin hira da shugabannin kungiyar Arewa Consultative Forum (ACF) a fadarsa da ke Abuja, cewar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Har ila yau, ya godewa duka ministocinsa da masu mukamai sai dai ya ce duk wanda ya gaza, zai raba shi da kujerarsa, Daily Post ta tattaro.
"Ina godewa duka ministocina da irin kokarin da suke yi, sai dai kuma duk lokacin da na fahimci sun gaza wurin bautawa ƴan Najeriya zan kore su."
- Bola Tinubu
'Gwamnoni na samun kudi" - Shugaba Tinubu
Tinubu ya roki gwamnoni da su inganta rayuwar al'umma musamman wurin amfani da kudin kananan hukumomi da gaskiya yadda ya dace.
"Ina rokonku da ku kira gwamnoni, ina iya bakin kokarina wurin tabbatar da samar da kudi ga Najeriya."
"Dole su ma su tausaya wurin duba zuwa ga mutane da ke karkashinsu a wannan lokacin."
- Bola Tinubu
Tinubu zai sake gabatar da kasafin kudi
A wani labarin, kun ji cewa Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu zai gabatar da karin kasafin kudin 2024 ga Majalisar Dokokin kasar nan.
Shugaban ƙasar ne ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi a zaman haɗin guiwa a zauren majalisar datttawa ranar Laraba, 29 ga watan Mayun 2024.
Wannan na zuwa ne yayin da ƴan kasar ke kokawa kan halin kunci da tsadar kayayyaki da ake fama da shi musamman na abinci.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng