Gwamnatin Jihar Sokoto Ta Rufe Hotel da Ake Yada Ayyukan Barna

Gwamnatin Jihar Sokoto Ta Rufe Hotel da Ake Yada Ayyukan Barna

  • Gwamnatin Sokoto ta tabbatar da rufe Ifoma hotel bayan zarginsu da zama matattarar yada ayyukan barna a fadin jihar
  • Har ila yau gwamnatin ta kara da cewa rufe hotel din ya biyo bayan kiraye-kiraye da suka samu daga mutanen garin Sokoto
  • Kwamishinoni da manyan jami'an tsaron jihar ne suka dira Ifoma hotel bayan samun bayanan sirri kan barnar da ake yi a ciki

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Sokoto - Gwamnatin jihar Sokoto ta sanar da rufe hotel din Ifoma da ke cikin jihar bisa zargin aikata ayyukan barna.

Gwamnan jihar, Ahmed Aliyu Sokoto ne ya bayar da umurnin kulle hotel din biyo bayan korafi da al'ummar garin suka shigar.

Kara karanta wannan

'Daɗi zai biyo baya' Masana sun fadi dalilin goyon bayan tsare tsaren Tinubu

Sokoto
Gwamnati ta rufe hotel saboda yada badala a Sokoto. Hoto: Office of the Commissioner, Ministry for Religious Affairs, Sokoto State.
Asali: Facebook

A bayanan da ma'aikatar harakokin addini ta wallafa a shafin ta na Facebook an gano cewa an rufe hotel din ne har illa ma shaa Allahu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamitin da suka rufe Ifoma hotel a Sokoto

Gwamnan jihar ya kafa kwamiti mai karfi da suka jagoranci kulle hotel din ciki har da kwamishinan harkokin addini, Dakta Jabir Sani Mai Hula.

Har ila yau cikin kwamitin akwai kwamishinan ciniki da masana'antu, Haruna Abbas Bashar da manyan jami'an tsaron da suke aiki a jihar.

"Abin da yasa aka kulle Ifoma hotel" - Sokoto

Duk da cewa ba a ayyana dalilin rufe hotel din ƙarara ba, amma kwamitin ya ce ana aikata abubuwan da ba su da ce ba a hotel din.

Har ila yau, kwamitin ya kara da cewa a makon da ya gabata an samu rahoton mutuwar wata yarinya a hotel din.

Kara karanta wannan

Kano: An shiga ɗimuwa bayan jin harbe harbe a fadar da Aminu Ado Bayero yake

An kafa jami'an tsaron jiha a Sokoto

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Sokoto ta kaddamar da sabuwar rundunar tsaron al'umma, domin taimakawa sauran jami'an tsaro.

Da ya ke rattaba hannu kan dokar kafa rundunar tsaron, Gwamna Aliyu ya ce rundunar tsaron ba kishiyar 'yan sanda ba ce kawai za su taimaka wajen dakile barna ne.

Gwamnan jihar ya kuma ce wannan matakin zai taimakawa gwamnatin Shugaba Tinubu ya tabbatar da tsaron rayuka da dukiyar al'umma.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel