An ba Gwamnati Shawarar Karya Farashin Dala, Watakila Farashin Kayan Waje Ya Sauko

An ba Gwamnati Shawarar Karya Farashin Dala, Watakila Farashin Kayan Waje Ya Sauko

  • Kwamitin shugaban kasa a kan manufofin kasafin kudi da sauya fasalin haraji ya ba gwamnatin tarayya sanya harajin Dalan kayan da ake shigowa da su a kan N800
  • Shugaban kwamitin, Taiwo Oyedele ya shaidawa manema labarai cewa sun bayar da shawarar ne ganin yadda hauhawar farashin dala ke janyo rashin daidaito kan harajin
  • Ya ce lokacin da suka yi kasafin kudi ana canza dala a kan N800 amma yanzu ya karu zuwa N1,000 zuwa sama, suna fatan a amince da kudin harajin da suka nema

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Lagos-Kwamitin da shugaban kasa ya kafa kan manufofin kasafin kudi da sauya fasalin haraji ya ba gwamnatin tarayya shawara kan sabon haraji kan kayan da ake shigowa da su kasar nan.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu na shirin gabatar da ƙarin kasafin kuɗin 2024 a majalisar tarayya

Kwamitin ya ce kamata ya yi gwamnati ta amince da canjin N800 kan kowacce dala a matsayin harajin kayyakin da ake shigowa da su Najeriya.

Bola Tinubu
Kwamitin gwamnatin tarayya kan haraji ta nemi sassauta harajin kayan da ake shigowa da su Najeriya Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

The Cable ta wallafa cewa shugaban kwamitin, Taiwo Oyedele, ne ya bayyana hakan a lokacin da yake yiwa manema labarai bayani kan ayyukansu a jihar Lagos.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce akwai damuwa matuka idan aka lura da yadda kudin harajin shigo da kaya lasar nan ke sauyawa wanda tabarbarewar kasuwar canji ke haddasawa.

'Hauhawar farashi na kawo cikas,' Oyedele

Shugaban kwamitin kan manufofin kasafin kudi da sauya fasalin haraji, Taiwo Oyedele ya bayyana yadda hauhawar farshin dala ke kawo cikas ga samar da tsayayyen haraji, kamar yadda Vanguard News ta wallafa.

Yanzu muna rokon gwamnati a kan batun shigo da kaya kasar nan, ta sanya hannu kan dokar cewa N800 ne kan kowacce dala har zuwa watan Disamba.

Kara karanta wannan

'Daɗi zai biyo baya' Masana sun fadi dalilin goyon bayan tsare tsaren Tinubu

An samu labarin yawan sauye-sauyen kudin haraji daga hukumar hana fasa-kwauri ta kasar na inda ya bayyana fatan Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai karbi lamarin.

CBN ya amince bankuna su ciri haraji

A baya mun kawo muku labarin cewa babban bankin kasar nan ya amince bankunan kasar nan na ciri haraji kala-kala da akalla suka kai biyar idan aka yi hada-hada ta kafar intanet.

Legit Hausa ta tattaro daga cikin harajin da bankunan ke cira akwai na tura kudi, buga hatimi, da harajin sakon kar-ta-kwana da kuma na kimar hada-hada (VAT).

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.