Gwamna Ya Rabawa Mutane Sama da 5,000 Takardar Ɗaukar Aiki a Arewa

Gwamna Ya Rabawa Mutane Sama da 5,000 Takardar Ɗaukar Aiki a Arewa

  • Gwamna Umar Namadi ya ce gwamnatinsa ta ɗauki sababbin malamai domin cike giɓin da ke akwai a ɓangaren ilimi a jihar Jigawa
  • Namadi ya ce ilimi na ɗaya daga cikin manufofi 12 da gwamnatinsa ta sa a gaba da nufin ɗaga darajar jihar ta ƙara ɗaukaka
  • Shugaban hukumar ilimin bai ɗaya ta jihar ya ce sababbin malaman da aka ɗauka sun shafe shekara biyu suna aikin wucin gadi kafin a ɗauke su aiki

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Jigawa - Gwamnan jihar Jigawa Umar Namadi ya raba takardar daukar aiki ga sababbin malamai 3,143 da wasu sababbin ma'aikata 2,445 a faɗin jihar.

Gwamna Ɗanmodi ya rabawa sababbin waɗanda suka samu aikin takardun shaidar ɗaukar aiki a wani taro da aka shirya a ɗakin taron Malam Aminu Kano a Dutse.

Kara karanta wannan

Majalisa ta ɗauki mataki kan korar daraktoci da manyan ma'aikata a bankin CBN

Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa.
Gwamnatin Jigawa ta dauki malamai 3,143 da wasu ma'aikata 2,445 Hoto: Umar Namadi
Asali: Twitter

Namadi ya ce samar da aikin yi na ɗaya daga cikin kudirinsa na aiwatar da ajandoji guda 12, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin ɗaukar malamai aiki a Jigawa

Gwamnan ya ce babu wata manufar gwamnati da za a iya aiwatar da ita yadda ya kamata ba tare da isassun kwararrun ma’aikata ba.

"Manufofinmu guda 12 da muka tsara da nufin daukaka jihar Jigawa, sun hada da samar da ingantaccen ilimi ga daukacin yaran jihar.
"Don cimma wannan, dole ne mu cike gibin malamai, shiyasa muka ɗauki wannan adadi na malamai a yanzu, kuma za mu ci gaba da yin haka har sai mun sami malami a kowane aji."
"Noma na sahun gaba a manufofimu, mun tsara samar da ayyukan yi, kawar da talauci, samun wadatar abinci, gina ingantaccen ci gaban tattalin arziki mai dorewa."

Kara karanta wannan

Hajjin 2024: Allah ya yiwa wani Alhaji daga Najeriya rasuwa a Makkah

- Gwamna Umar Namadi

Yadda aka ɗauki malamai a Jigawa

Shugaban hukumar ilimin bai daya na jihar Jigawa, Farfesa Haruna Musa, ya bayyana cewa malaman da aka ɗauka aiki sun yi aikin koyarwa na wucin gadi tsawon shekaru biyu.

Ya ce bayan ɗaukar wannan lokaci suna aikin wucin gadi, an lura cewa sun dace a ɗauke su aiki na dindindin bayan cin jarrabawar gwajin da aka shirya masu, Tribune Nigeria ta rahoto.

Aminu Majeh, wani malamin makaranta a Birnin Kudu ya ce Gwamna Namadi ya ɗauko hanyar magance matsalolin ɓangaren ilimi.

Ya shaidawa wakilin Legit Hausa cewa babbar matsalar da ake fuskanta a firamare da sakandire ita ce ƙarancin malamai, kuma Ɗanmodi ya fara lalubo bakin zaren.

Ya ce:

"Wannan ba ƙaramin ci gaba bane a harkar ilimi, waɗanda aka ɗauka suna da kwarewar koyarwa. Sannan bayan ɗaukar su aiki, an sake ɗaukar malaman wucin gadi.
"Karancin malamai ne babbar matsalar ilimin matakin farko kuma ga dukkan alamu gwamnati ta ɗauko hanyar magance matsalar "

Kara karanta wannan

"Yan bindiga sun fara kai hari da manyan bindigu," Gwamna Raɗda ya tura saƙo ga Tinubu

Tinubu zai gabatar da ƙarin kasafin 2024

A wani rahoton kuma Bola Ahmed Tinubu na shirin gabatar da ƙarin kasafin kudin 2024 ga majalisar wakilan tarayya nan ba da jimawa ba.

Shugaban ƙasar ne ya bayyana haka a jawabinsa ga mambobin majalisar yayin zaman haɗin guiwa ranar Laraba, 29 ga watan Mayu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262